Wa hana "Visa" ta shiga Nijar zai shafa?
August 27, 2025
Wannan mataki da Nijar din ta dauka dai, ya shafi kasashe biyar na Tarayyar Turai da kuma Ingila. Ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar ta Nijar ce dai ta bayyana wannan mataki na matsalolin da 'yan Nijar ke fuskanta wajen samun takardar izinin shiga Turai a birnin Yamai, wanda hakan ke tilasta musu neman takardar "Visa" zuwa Turai yin balaguro zuwa kasashe makwabta. Dangane da haka ne Nijar din ta dakatar da bayar da "Visa" a ofisoshin jakadancinta da ke kasashen Italiya da Jamus da Holland da Belgium da Birtaniya, inda sai dai 'yan wadannan kasashe su je birnin Geniva na kasar Switzerland ko Ankara na Turkiyya ko kuma su je birnnin Moscow na kasar Rasha.
A yanzu ofisoshin jakadancin Nijar din na wadannan birane ne kawai, ke da izinin bayar da "Visa" ga 'yan kasashen da Nijar din ta shafawa bakin fenti. Seidik Abba dan jarida ne dan asalin Jamhuriyar Nijar mai sharhi kan harkokin tsaro da siyasar kasa da kasa, a cewarsa matakin ba kowa da kowa zai shafa ba.
Duk da cewa hukumomin na Nijar sun sanar da hanyoyin da suka bi kafin daukar wannan mataki na mayar da martani ga wasu kasashen na Turai, ga wasu 'yan Nijar din da ke zuwa kasashen na Turai suna dawowa kuma suke mu'amula da al'ummar Turai ba cikin matsala ba duk da matakin bai sabawa ka'ida ba daukar sa zai takura wa wata al'umma musamman ta Turai.
Sai dai wasu na ganin cewa a tsari na tafiyar kasa musamman wacce ke cikin fafutuka ta neman 'yanci da kare mutuncinta, matakin da Nijar din ta dauka na ramuwar gayya ko mayar da martani shi ne zai iya kasancewa yare ko harshen da su wadannan kasashen za su ji su kuma fahimta har ma a zauna domin tattaunawa kamar yadda dan jarida Seidik Abba mai sharhi kan harkokin tsaro da siyayar kasa da kasa ya nunar. A halin yanzu dai dangane da masu bukatar takardar "Visa" ta diflomasiyya ko ta ma'aikata, ofishin jakadancin Nijar da ke birnin Brussels na kasar Beljiyam ne ke da alhakin bayar da ita ga wadannan kasashen kamar yadda sanarwar ofishin ministan harkokin wajen kasar ta Nijar mai dauke da sa hannun minista Bakary Yaou Sangaré ta nunar.