Tchangari zai shaki iskar 'yanci a Nijar?
October 15, 2025
Gidan kurkukun na Fillingue da aka tsare dan fafutukar na Jamhuriyar Nijar Moussa Tchangari na da nisan kimanin kilomita 180 da Yamai babban birnin kasar, inda ake zargin sa da laifukan da suka shafi hada baki da wasu manyan kasashe da kuma goyon bayan masu ayyukan ta'addanci. Sai dai tuni makusantan Tchangari ke kallon wannan zaman sauraren a matsayin babban ci-gaba da ka iya kai wa ga sallamar dan farar hular, muddin ba a same shi da wani laifi ba.
Abin farin ciki ne
An dai kai shugaban kungiyar farar hula ta Alternative Espace Citoyen Tchangari zuwa birnin Yamai daga, inda ake sauraron shari'ar a matsayin mataki na farko na kai wa ga shari'a da za ta bayar da damar yanke hukuncin ko ya aikata laifukan da aka zarge shi da su ko bai aikata ba. Ga dai abin da wani dan uwansa mai suna Honorable Kiari Moustapha ke cewa: "Wannan sauraro abun farinciki ne a gare mu, domin zai bai wa alkali damar sanin gaskiyar lamari..........."
'Yan uwa da abokan arzikin Tchangari da sauran 'yan kungiyoyin farar hula sun halarci zaman kotun, domin nuna goyon bayansu gare shi kan halin da ya tsinci kansa a ciki. An dai kama shi ne, tun bayan dawowarsa daga wani bulaguro da ya kai shi kasashen Cote d'Ivoire da babban birnin Tarayyar Najeriya Abuja. Tsare Tchangari dai, ya kasance wani babban kalubale ga iyallansa da 'yan uwansa da ma abokan aikinsa.
Mutane sun samu damar ganin dan fafutukar
A makon da ke tafe ne za a sake mayar da Tchangari zuwa Yamai gaban kuliya, domin ci gaba da sauraron shari'ar. Shi da kansa dai ke cewa da mutane su koma gida ko wuraren aikinsu, domin mataki ne na sauraro kawai. Sai dai hakan ya kasance wata dama ga wadanda suka jima ba su ga dan farar hular ba, inda suka sa shi a idanunsu cikin sauki ba tare da sun je yankin Arewa maso Gabashin kasar ta Nijar da aka tsare shi ba.