Ko za a aiwatar da karin albashi a Nijar?
October 23, 2025
An dai jima ana kai ruwa rana tsakanin kungiyoyin kwadagon kasar da gwamnati a kan batun karin mafi kanrancin albashin, inda hambarariyar gwamnati ta amince da bukatar kafin juyin mulki inji Issa Mahamadou na kungiyar FESYNAF ta kananan ma'aikata a matakin jiha.
Su wa karin albashin ya shafa?
Akasarin kananan ma'aikatan dai sun hadar da leburori da kuku da direbobi da makamantansu, wadanda suka kasance ma'aikatan gwamnatin da kuma tsadar rayuwa ke tasiri sosai a kansu inji Abdulaziz Jawo wani lebura da ke aiki a wata ma'aikatar gwamnati.
Shi kuwa Lawaly Mahaman Salisu jagoran kungiyar kananan ma'aikatan jami'o'in Nijar ta SYMPATUT ya nunar da cewa: "Matakin abun alfahari ne, ganin yadda zai taimaka wajen kyautata rayuwarsu. Koda yake a Nijar ba a cika ganin gwamnatin na bayar da albashin da ke kasa da jaka 30 ga ma'aikatanta ba.
A ina matsalar ta fi kamari?
Sau tari dai, ma'aikatu masu zaman kansu ne ke biyan albashi kadan a Njar. "Dole ne dai gwamnatin ta sa ido, duk da cewar ita da kanta na fuskantar matsalar albashi," a cewar Issoufou Souley Sherif mai magana da yayun hadadiyar kungiyar kwadago ta CNT. Kallo dai ya koma ga ma'aikatu masu zaman kansu kamar kafofin yada labarai, inda ma'aikatansu ke karbar albashin da bai taka kara ya karya ba.