Nijar: Kotu ta daure jagororin farar hula
March 27, 2018Talla
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta bukaci hukumomin Nijar su saki jagororin gwagwarmayar da ke tsare, a cewar kungiyar, ci gaba da tsare su zai haddasa sabuwar rigima tsakanin fararen hula da jami'an tsaro.
Sai dai ministan harkokin wajen kasar Bazoum Mohammed ya ce kamen na kan ka'ida, ganin yadda aka haramta zanga-zangar saboda dalilai na tsaro.
Nijar dai na cikin kasashen yammacin Afirka da ke yawaitar fuskantar zanga-zanga, sai dai a Nijar din kungiyoyin farar hula na sa in sa da gwamnati kan sabbin tsare-tsaren da suka shafi karin harajin wayar salula.