1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Nijar: Kotun shari'ar 'yan kasa da gwamnati

Salissou Boukari
November 9, 2023

Shugaban mulkin sojin Nijar ya nada sabbin mambobin kotun kasa da ke hukunci tsakanin 'yan kasa da gwamnati.

Revisionsgericht in Niger
Hoto: DW/M. Kanta

Ita dai wannan kotu da ake kira Cour d'Etat wato kotun kasa, ta hade kotuna ne guda biyu da a baya suke rarrabe kuma kowace na cin gashin kanta, wato Conseil d'Eta da cour de Cassassion kotu mai kula da karya shari'a. Wasu dai na ganin koma baya ne hade kotunan biyu, amma kuma cikin wannan tsari na rikon kwarya za ta taimaka sosai domin a samu bangarori na shari'a su tafiyar da ayyukansu yadda ya kamata.

Shugaban mulkin sojin Nijar Abdourahamane TianiHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP

Da yake Magana kan kaddamar da mambobin kotun, shugaban kungiyar Stop Corrution mai yaki da cin hanci da rashawa Omar Adamou, ya ce samar da wannan kotu babban ci gaba ne sai dai abun da suke jira da ita shi ne ta yi aikinta na shari'a da gaskiya domin al'umma.

Karin Bayani: Bukatar yin gyara a fannin shari'ar Nijar

A baya dai gamayyar wasu lauyoyi matasa sun yi hannunka mai sanda dangane da yadda ya kamata sabbin hukumomin mulkin soji su yi dan ganin shari'a na gudanar da ayyukanta yadda ya kamata domin 'yan kasa su kiyaye hakkin da yake kansu wanda shari'a ta tanada inda suka ce ana kama mutane ana tsare su ba bisa shari'a ba.

Hoto: AFP/Getty Images

Abin jira a gani dai shi ne matakin da sabbin hukumomin za su dauka don ganin sun yi wannan aiki na yaki da rashin hukunta masu laifi da ake zargin gwamnatin da shude da aikatawa ta dalillai na siyasa, da yadda su kuma sabbin hukumomin za su yi aiki da bin ka'idoji na dokokin kasa da kasa.