Nijar: Kula da 'yan gudun hijira a Agadez
May 21, 2025
Shugabar kungiyar kuila da kaurar Jama'a ta duniya OIM da tawagar da ta mara masa baya , sun ziyarci sansanonin saukar bakin da ke cikin Agadez don gani da ido yadda aikin kula da yan gudun hijira ke gudana a jihar Agadez
Bakin hauren dai da yan gudun hijira a Agadez sun kasu kashi biyu, akwai wadanda ke cikin sansanin da kuma wadanda ke wajen sansanin da adadin su ya haura 2000. Mai martaba sarkin abzin elhadji Oumarou Ibrahim Oumarou da ke cikin tawagar gwamna ya jinjina wa kokarin hukumomin Agadez na karfafa zaman lafiya
A yanzu haka dai bakin hauren da aka koro daga kasashen Aljeriya da Libiya kuma suka shiga Agadez sun haura dubu bakwai. Yan gudun hijira su ma sun kai fiye da 2000. Duk da haka hukumomi sun dauki aniyar yi musu gyaran halin da tallafa wa rayuwarsu tare da taimakon masu hannu da shuni.