1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

'Yancin bakin haure a matsayinsu na 'yan Adam

Abdoulaye Mamane Amadou AMA(LMJ)
May 12, 2022

Kungiyoyin fararan hulla da ke kula da bakin haure a Jamhuriyar Nijar sun kammala taron bita kan kare hakin bakin haure da kiwon lafiyarsu a matsayinsu na ‘yan Adam.

Nijar Diffa | Mayar da bakin haure agidajensu
Bakin haure na kan hanyar komawa a gidajensu daga DiffaHoto: Gazali Abdou Tasawa/DW

Zaman taron ya kumshi kungiyoyin fararan hulla da masu hannu da shuni da kasashen waje masu wakilci a kasar Nijar domin sanin inda aka kwana dangane da batun bakin haure da ke bi ta kasar, tare da duba irin matakan da kungiyoyi ke dauka na kula da su da kuma fadakar da su da lura da hakkokinsu, baya ga taimaka musu idan har suna da matsala a fannin dokar kasar da suke ciki kafin su fice.

Domin kare hakkokin bakin hauren a matsayinsu na 'yan Adam. Kungiyoyin kula da bakin haure sun yi tsari na musamman inda suke bayar da horo ga kungiyoyi na jihohin da ake samun kwarar bakin hauren don ganin cewa an kula da duk wanda ya shigo an san halin da yake ciki.

Karin Bayani: An ceto wasu bakin haure a Italiya

Nijar tare da ban hannu kasashen Turai ta dauki kwararan matakai dangane da kwarar bakin haure da ke bin hamadar Sahara ta jihar Agadez domin zuwa kasashen Libiya da Algeriya ko kuma neman ketarawa zuwa Turai wanda kuma da dama suka rasa rayukansu.

Sau tari ana samun cece-kuce tsakanin kungiyoyin fararan hulla masu kula da bakin haure da kuma gwamnatin Nijar, inda gwamnati ke ganin cewa kungiyoyin basu bin yadda ita take so a wasu lokuttan, inda ake zarginsu da hadin kai da bakin haure.