1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Makomar zabe babu Hama Amadou

March 17, 2016

A Jamhuriyar Nijar wasu masana da masharhanta ke yi ta tsokaci kan yadda za a gudanar da zabe ba tare da Hama Amadou ba ganin cewar yana kasar waje inda ake masa magani bisa tsanantar rashin lafiyarsa.

Hama Amadou nigrischer Oppositionspolitiker
Hoto: DW/S. Boukari

Jim kadan bayan tabbatar da ficewar dan takarar kawancen jam'iyyun adawa kuma shugaban jam'iyyar Moden Fa Lumana Afrika da zai kalubalanci Mahamadou Issoufou na jam'iyyar PNDS a zagaye na biyu na zaben 20 ga watan Maris, inda ya fice zuwa Turai don neman magani saboda tsanantar rashin lafiyarsa. Masana da masharhanta a fannin dokokin kolin kasa da ma masu bita da bibiyar fagen demukradiyya ke cigaba da tsokaci kan yadda makomar zaben Nijar din za ta kasance a gaba.


Fannonin dai na wannan tsokacin ne duba da yadda ake ke shirin yin zabe a yayin da dan takara daya baya nan, inda hakan ke zama wani sabon abu irinsa na farko ga gaba dayan tarihin demukradiyyar Nijar mai shekaru sama da 25.

Masana kundin tsarin mulkin kasar na masu ganin duk da matsayin da 'yan adawar kasar suka dauka na janyewa daga duk wasu shirye-shirye da suka jibanci zabe, makale takarar Malam Hama Amadou da 'yan adawa suka yi ba tare da sun janyeta ba na iya taka muhimmiyar rawa a gaba domin kalubalantar sakamakon zabe.

Dan takara kadai ke iya kalubalantar zabe

Farfesa Jibril Abarchi malamin shari'a ne a jami'ar birnin Yamai da ya ce:

"Wanda yake dan takara shi kadai ne ke iya ja game da zabe kuma idan har yana dan takara, shi kadai ne ke kai karar sakamakon zabe a kotu. To idan ya janye bai iya kai karar a kotu."

Hoto: BOUREIMA HAMA/AFP/Getty Images


Duk da tasirin da janyewar 'yan adawar za ta yi ga masu bibiyar tafarkin demukradiyya ire-iren su Malam Lawali Aboubakar halin da ake ciki yanzu na yakin neman zabe ba tare da 'yan adawa ba na iya taka wata babbar rawa wajen ragewa shi kansa sahihancin zaben armashi.

"Wane irin zabe ne za a yi ka je cikin zauren zabe babu wakilin Hama Amadou a samu wakilin Mahamadou Issoufou ba tare da na Hama Amadou ba. To ka ga ke nan akwai kuma nan kundin ya ce sai an yi zaben nan tilas a ranar 20 ga wannan wata na Maris, to ka ga ke nan akwai sauran rina a kaba. To lalle idan wannan ya tabbata, to ka ga ke nan babu yadda za a yi zaben yayi armashi. kasan duk abinda aka yi a cikin gardama to kasa tana iya jinshi daga baya kuma idan haka ma ta tabbata to ina sheda maka da cewar ko da ma Hama Amadou ya sha kaye a zabe to da kyar ya je ya taya Mahamadou Issoufou murna a ganina."

Kokarin samun goyon baya daga dukkan bangarori
Ya zuwa yanzu dai wani babban kalubalen da ke gaban kowane bangare na masu adawa da na masu rinjaye shi ne na samun tarin goyon bayan jama'a da za su fito walau don jefa kuri'a ko kuwa su yi na'am da bukatar 'yan adawa a ranar zabe inji masu sharhi.

Hoto: DW/M. Kanta

Duba da yadda 'yan adawa suka saka kira ga magoya bayansu da su kaurace wa zuwa zabe, a yayin da kawancen masu mulki ke sanya kira ga magoya bayansu da su fito don tabatar wa Mahamadou Issoufou kwarin guiwar yin kayen da kawancen da ke mara masa suka kira kayen reni. Har yanzu ga Malam Lawali Aboubaka.
"Ko su fito da yawa ko kada su fito da yawa, to idan sun fito da yawa to kaye ya yi tasiri, idan ko ba su fito da yawa ba kayen ke nan bai yi tasiri ba. Ka san Nijar ta zamo wata "laboratoir" da ake cewar ana sarrafa demukradiyya, to amma matsalar "laboratoir" shi ne wani lokacin tana sarrafa abu mai kyau wasu lokutan kuma sai a sarrafa lalata."


Wannan lamarin dai na takon-saka tsakanin 'yan adawa da na bagaren masu mulki na zuwa ne a yayin da kowane bangare ke cewa ya lura da take-taken wancan na neman karewa da shi, inda masu mulkin ke ganin 'yan dubaru ne 'yan adawa ke yi don kai kasar ga shiga wani yanayi na karshen wa'adin shugaba Issoufou ba tare da zaben shugaban kasa ba, abin da suka ce ya saba wa kima. A yayin da 'yan adawar ke cewar masu mulkin na nema ne su yi amfani da karfin iko don karyawa inda ba gaba. Komai take ciki dai Hausawa na cewa rana ba ta karya sai uwar diya ta ji kunya.