Martani kan ayyukan ci-gaba a Nijar
December 2, 2020Gwamnatin ta Mahamadou Issoufou dai ta ce an samu ci gaba a fannoni da dama, kamar na yaki da cin hanci da inganta rayuwar al'ummar karkara da fannin tattalin arziki da dai sauransu. Gwamnatin ta Nijar ta ce a fannin tattalin arziki Nijar ta samu ci-gaba mai yawa a shekaru 10 na baya-bayan nan a karkashin shirin nata na gina kasa da aka fi sani da "Programme de la Renaissance."
Karin Bayani: Taro kan yin zabe cikin lumana
Gwamnatin ta ce tattalin arzikin Nijar ya karu a takaice sama da kaso biyar cikin 100, wannan kuwa duk da tarnakin da annobar COVID-19 ta janyo ga tattalin arzikin kasar a bana. Sai dai Alhaji Yakuba Dan Maradi shugaban kungiyar 'yan kasuwar Nijar masu shigo da haja daga waje, ya ce zahirin abin da 'yan kasuwar ke gani ya sha bam-bam da alkaluman na gwamnati.
Karin Bayani: Tarnaki a yaki da cin hanci a Nijar
Wannan fanni da gwamnati ta ce an samu ci gaba shi ne na yaki da cin hanci da rashawa. Sai dai a nan ma kungiyar Transparancy Internatioanal mai yaki da cin hanci a duniya reshen Nijar din, ta bakin magatakardanta malam Maman Wada cewa ya yi lallai gwamnatin ta dauki matakai iri-iri a saman takarda, amma ba ta yi aiki da su a zahiri ba.
Gwamnatin ta kuma nunar da cewa a tsawon shekaru 10 rayuwa mutanen karkara ta inganta, kana talauci ya ja baya a yankunan na karkara. To amma Abdou Naino Gajamgo shugaban kawancen kungiyoyin manoma da makiyaya da aka fi sani da FENAP ya ce rayuwar mutanen karkarar ba ta sauya ba a wadannan shekaru 10 a karkashin tsarin na "Programme de la Renaissance."
Karin Bayani: Bankado badakalar cin hanci a harkar mai a Nijar
Kazalika gwamnati ta ce shirin ya inganta harkar ilimi da kiwon lafiya a birane da kauyuka. Sai dai kuma Malam Musa Cangari na kungiyar Alternative ya ce kudin da gwamnatin ta rinka warewa wadannan fannoni biyu a shekaru 10 na baya-bayan nan, na nuni da sabanin abin da gwamnatin ke ikirari. Gwamnatin dai ta kuma zano manyan ayyukan gina hanyoyin mota da birane da kauyuka, kana Nijar ta kafa bajintar ci gaba da haramtawa kungiyoyin 'yan ta'adda mallakar ko da murabba'i guda ne na fadin kasar, kana kimar Nijar ta daukaka a idanun duniya, inda ta karbi bakuncin manyan tarurruka da suka hada da na kungiyar kasashen Musulmi ta OIC a baya-bayan nan.