1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: An sallamo wasu tsofin ministocin gwamnatin Bazoum

Gazali Abdou Tasawa AH
July 30, 2024

An saki wasu ministoci hudu daga cikin manyan jami'an hambararriyar gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum da ake tsare da su tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin 2023.

Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

 Hukumomin mulkin sojan sun gurfanar da manyan jami'an hambararriyar gwamnatin sama da 10 ne a gaban kuliya a bisa zargin su da aikata laifuka da dama da suka hada da na cin amanar kasa. Yanzu haka dai lauyan tsoffin ministocin hudu wato tsohon ministan makamashi kana shugaban jam'iyyar kishin kasa,Ibrahim Yacouba, da tsohon ministan fasali Dokta Rabiou Abdou da Dokta Ahmed Jidoud tsohon ministan kudi da Dr Hama Adamou Soule tsohon ministan cikin gida dukkaninsu ‚ya'yan jam'iyyar PNDS Tarayya, da kotu ta ba da umurnin sakin su tuni da suka isa gidajensu. Da yake tsokacin matakin kotun Malam Assoumana Mahamadou na jam'iyyar PNDS Tarayya ya ce matakin zai taimaka ga sanyaya fagen siyasar kasar da kuma hada  kan kasa.

'' Muna wa Allah godiyya da ya nuna mana wannan rana ta fara sakin abokanmu wadanda aka kama bayan juyin mulki. Abin alfahari ne. Kuma muna fatan su ma sauran abokananmu da ke tsare za a sake su. Sannan ina ba da shwara ga sojojin da suka kwaci mulki da cewa wannan dama ce ta samu ta su yi shawara da kowa da kowa kamar yadda suka ce dan hada kan kasa cikin wannan hali da Allah ya kawo mu ciki ''

Hoto: Presse- und Kommunikationsdienst der Präsidentschaft von Niger

To sai dai wasu ‚yan Nijar din na ganin sakin wadannan mutane ba za iyi wani tasiri ga shawo kan rikicin kasar ba, matukar hambararren shugaban kasa Bazoum Mohamed na ci gaba da kasancewa a tsare. Malam Siraji Issa na kungiyar MOJEN na daga cikin masu irin  wannan ra'ayi.

''To ai da ma wadannan mutane ba a kama su ba a kan ka'ida ba, aka kai su kurkuku aka rufe. Dan haka sakin wadannan mutane a yau babu wani tasiri da zai yi. Amma abin da na gano shi ne sojojin nan suna son samun goyon bayan wadannan mutane da suka saki. To amma idan ba tsohon shugaban kasa Mohamed Bazoum aka sako ba, to ina ga a nan dai gidan jiya noman goje kuma tamkar an bira ne ba a fado ba''

Hoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

To amma Malam Mahamadou Gamatche wani dan fafutika a Nijar, na ganin akwai bukatar fadada matakin bayar da belin ga wasu sojojin da ake tsare su shekaru da dama, idan ana son cimma burin hada kann 'yan Nijar a cikin sabuwar tafiya.

''Yanzu ga zancen da ake akwai sojoji da yawa wadanda aka kama wancen tsohon mulki. Kuma mun yi imanin ba bisa kann gaskiyya ba ne, amma saboda dalilai na siyasa ne´ya kamata a sake su suma.

Hoto: Balima Boureima/Reuters

Yanzu haka dai ko baya ga wadannan ministoci hudu akwai wasu manyan kusoshin tsohuwar gwamnatin irin su Malam Foumakoy Gado, da Mahaman Sani Mahamadou tsohon ministan man fetur kana da ga tsohon shugaban kasa Mahamadou Issoufou da tsohon ministan tsaro Malam Kalla Moutari da ake sa ran kotun za ta  sallama  a nan gaba.