1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Martanin MNSD ga sabuwar jam'iyyar MPR

Abdoulaye Mamane Amadou/GATOctober 12, 2015

Jam'iyyar MNSD Nasara ta ce Allah ya raka taki gona da matakin kafa sabuwar jam'iyya da tsaffin 'yan tawayenta suka kafa a karkashin jagorancin Albade Abouba

Alhaji Seini Oumarou shugaban jam'iyyar MNSD Nasara ta adawa a Nijar
Alhaji Seini Oumarou shugaban jam'iyyar MNSD NasaraHoto: MNSD

A Jamhuriyar Nijer 'yan awoyi kalilan bayan bangaren Alhaji Albade Abouba wanda ya jima yana jayayya a jamiyyar adawa ta MNSD ya kafa tasa jamiyyar biyo bayan kayin da ya sha a gaban kotu, babbar jamiyyar ta adawa ta ce Allah raka taki gona ga tsoffin 'yan twayenta, amma ta ce kofofinta a bude su ke domin sake karbar tsaffin bijirarrin 'ya'yan nata idan suka amince da su yi nadama.

A yayin wata firar da yayi da tashar DW hausa ne dai mataimakin shugaban jamiyyar adawar ta MNSD Nasara kuma jigo a reshenta na jihar Maradi Alhaji Ali Sabo ya nuna gamsuwa da matakin da bangaren na Albade Abouba ya dauka na kafa tasa jamiyyarsa bayan shafe tsawon shekaru biyu ana kai ruwa rana tsakanin bangarorin biyu wanda da kyar da sudin goshi kotu ta kai ga yanke hukumcin. Mataimakin shugaban jamiyyar dai ya zargin bangaren Albade Abuba da taka wata muhimmiyar rawa wajan tsarin wargaza jamiyyar ta adawa domin kurum abin da ya kira barin Shugaban kasa Issoufou Mahamadou shi kadai ya samu damar kai labari a zaben shugabancin kasa da zaa yi a farko farkon watan Febrarun sabuwar shekara.

MNSD ta ce Allah raka taki gona da kafa jam'iyyar MPR

" Duk wannan kokowar da ka gani wannan abin da aka ma MNSD Nasara, zamansu na tsutsa cikin goro da suka ma mu wannan kokowar da aka sa su yi, Mahamadu Isufu ya saka su yi ta. Yanzu kamar gona ce idan ka fidda mata tsambare bunkasuwa take. Na tafiya sun tafi wannan ko dimun akwai rasuwa akwai haihuwa cikin duniya kuma mun san yau abin da aka sakasu a ciki don su wargaza Nijar ne mun sani, don Isufu ya samu waadi na biyu ne tunda da sun fito da dan takara a zaben shugaban kasa mai zuwa da mun masu kirari mun ce diya ne "

A nasu bangare kwa kusoshin jamiyyar ta MPR Jamhuriya cewa suka yi duk wasu kalaman suka ko rudani tsakanin bangarorin biyu nasu da na jamiyyar MNSD mai adawa sun riga sun kare, babban abin da ke a gaban sabuwar jamiyyar shi ne na kafata tare da bata sabuwar alkibla. Alhaji Ibro Ayouba kakakin jamiyyar MPR jamhuriya ne mai jagorancin Albade Abouba.

Alhaji Seini Oumarou shugaban jam'iyyar MNSD NasaraHoto: DW/M. Kanta

Jam'iyyar MPR ta mayar da hankali ga aikin kafuwarta a cikin kasa

" Tsakaninsu da mu yanzu sai dai hulda ta jamiyya da jamiyya irin wadda za mu yi da ko wace jamiyya. In kana jayayya ne da mutun za ka samu ya gaya maka wata magana ko ka gaya mashi. Amma yanzu mu gabanmu aikin mai yawa ne ko da yake tsoffin tutoci ne zaa janyewa a saka sabbi kawai"

A yayin wani taron manema labarai da madugun 'yan adawar kasar ya kira kuma Shugaban jamiyyar ta Mnsd mai cikakken 'yanci a yanzu Alhaji Seini Oumarou ya tabo batun tsoffin magoya bayan nasu da cewar kofofin MNSD na bude ga duk wadanda suke bukatar dawowa idan sun gano da cewar sun fada kuskure.

Seini Oumarou ya yi tayin kome ga tsaffin 'yan tawayen jam'iyyarsa

"Gaskiya ne halin da tsoffin abukanin tafiyarmu suka nunawa jamiyyar ya yi muni sosai to amma sai dai kamar yadda muke fadi ne da cewar duk wadanda suka ga suna da niyyar dawowa da zuciya daya idan har suka gano da cewar an yi masu wani dabo ne to muna tarbonsu da hannu biyu biyu domin gina jamiyya"

Sai dai batun dawowar gida da madugun 'yan adawar ke yi wa tsaffin abukanin tafiyar sun kasance tarihi in ji kakakin jamiyyar MPR jamhuriya ta Albade Abouba Alhaji Ibro Ayouba.

" Wannan sai dai a saka shi cikin tarihi domin babu wata dama a ce a yi wata gyara. Tare ne ake, zaa zauna tare da zaa yi duk wani abin da zai samu na alkhairi"

A tsakiyar watan Agustan shekara ta 2013 ne dai rikici ya barke a cikin wasu manyan jamiyyun siyasa sakamakon anniyar shugaban kasa ta kafa wata gwamnatin hadin kan kasa wacce ta bar baya da kura a cikin manyan jamiyyun siyasar da suka jima suna kai ruwa rana a kotu. Cikin wadanda suka fada wanan matsalar har da babbar jamiyyar adawa ta MNSD, Jamiyyar da shugabanta ya ce ko ta halin kaka za su kalubalanci shugaban kasa a zaben farko na shugabancin kasa da zaa yi a cikin watan febraru na sabuwar shekara

Albade Abouba shugaban jam'iyyar MPR JamhuriyaHoto: DW/M.Kanta
Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani