1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mata dogarai a fadar sarkin Dogarawa

Lateefa Mustapha Ja'afar AA/SB
September 10, 2018

Shirin Abu Namu na wannan makon ya yi tattaki ne zuwa Jamhuriyar Nijar domin tattaunawa da matan da suka kasance dogarai a fadar sarkin Dogarawa na cikin jihar Tahoua.

Palast des Emirs von Damagaram in Zinder, Niger
Masarautar Haussa a NijarHoto: DW/M. Kanta

Matan ne dai suka nuna sha'awarsu ga shiga aikin na dogari a fadar masarautar garin Dogarawa da ke cikin jihar Tahoua. Sanin kowa ne dai a kasar Haussa Dogarai suke da alhakin kula da kare lafiyar sarakuna da ma kamowa, tare da gurfanar da mai laifi a fadar sarki. Baya ga haka mafi akasarin dogaran, kan kasance maza yayin da mata ke yin aiki na jakadiya. Sai dai a garin na Dogarawa da ke Jamhuriyar Nijar, matan sun zaburo tare da shiga wannan aiki na dogari, inda aka samu matan da suka kasance dogarai a fadar sarkin Dogarawa da ke Jamhuriyar Nijar.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW