Kalubalen matasan Nijar a Mali
November 5, 2025
'Yan ta'addan na kwacewa matasan kudin da suke samu, abin da suka ce yana tilasta wasu da dama daga cikinsu da ba su da kudin komawa gida makalewa cikin halin ha'ula'i. Ana iya cewa sannu a hankali zuwa ci-rani wajen ko buda da matasa da dama 'yan Nijar ke yi zuwa kasar Mali na zama wani babban kalubale, sakamakon tarin matsalolin da suke fuskanta.
A birnin Yamai dai a tashshin mota da masu zuwa yanki Gao na kasar Mali, mafi yawan matasan da suka koma gidan na cikin mawuyacin hali. Daga Nijar dai daruruwan matasa daga jihohin Damagaram da Maradi da Tahoua da Tillabery, sune suka fi yawa daga cikin masu zuwa neman zinare a Mali. Salissou wani matashi da shi ma ya koma gida daga kasar ta Mali ya ce, idan ka yi dace zaka samu alkhairi sosa a iakin hakar zinaren. Sai dai ya ce da suna da abin yi a gida Nijar, ba za su rinka tafiya ci-ranin ba, sabota tarin kalubalen da ke cikin aikin.