'Yan ta'adda sun addabi kauyukan jihar Tahoua
December 7, 2022Mazauna arewacin jihar Tahoua ta Jamhuriyar Nijar na ci gaba da kokawa bayan daukar dogon lokaci suna fuskantar barazana daga wasu kungiyoyi masu ikirarin jihadi da ke zuwa wajensu karbar kudin diyya ko kuma haraji. Jama'an da ke yankin sun shaida wa DW cewa ko da mutum ba shi da kudi, 'yan bindigar kan tilasta masa ba su kyutar dabbobi a matsayin kudin harajin da ya kamata ya biya su. Malam Yahuza da ke zaune a yankin ya ce ''hatta ciyawar da muke bai wa shanu, 'yan bindigar kan bukaci mu ba su.''
Wannan barazanar da mutanen yankin ke fuskanta ta kai ga shugaban Jamhuriyar Nijar, inda a shekarar da ta gabata ya kawo wata ziyara a yankin da zummar karfafa runduna ta musamman a yankin. Sai dai kuma masana na cewa kasancewar kasar na da fadin gaske har yanzu tsugune ba ta kare wa mazauna yankin ba.
'' An samu saukin hare-hare, amma duk da haka 'yan bindiga na karbar kudin fansa a wajen jama'a.'' in ji Malama Aishatu Takanamat
A cikin makon nan ne dai ministan kula da harkokin cikin gida na kasar ya kai ziyara a yankin na Tahoua domin duba halin da jama'a ke ciki bayan matakan tsaron da gwamnati ta dauka a bara. Wani mazaunin Mahamadu Natchiou yankin ya ce kafin gwamnati ta kawo sojoji a wannan yankin nasu, sun shiga cikin zulumi. A cewarsa, yanzu sun kuduri tallafa wa jami'an tsaro domin tabbatar da dorewar zaman lafiya.