1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Nijar mazauna waje za su yi zabe

Salissou Boukari LMJ
September 16, 2022

Hukumar Zabe mai Zaman Kanta a Jamhuriyar Nijar wato CENI, ta tattauna da 'yan jarida da ma kungiyoyin fararan hula domin bayar da bayani kan halin da ake ciki dangane da shirin kidayar 'yan Nijar da ke kasashen waje.

Nijar | Yamai | CENI | Zabe
Shlkwatar Hukumar Zabe mai Zaman Kanta a Nijar, CENIHoto: DW/A. Adamou

Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Jamhuriyar ta Nijar wato CENI dai, na fatan bai wa 'yan kasar da ke ketare damar yin zaben 'yan majalisar dokoki na cike gurbi da zai ba su damar samun wakilansu a majalisar dokoki. A karkashin kundin tsarin mulkin Jamhuriyar ta Nijar dai, mambobi 171 ne ya kamata su kasance a zauran majalisar dokokin kasar. Sai dai kuma an samu gibin guda biyar daga cikin wannan adadi, sakamakon wasu matsaloli da aka samu yayin zaben 'yan majalisar da ya gabata wanda ake ganin lokaci ya yi na cike gibin. Ya zuwa yanzu dai hukumar ta CENI, ta dukufa wajen gyaran takardunta domin ganin sun dace da wannan lokaci.

Akwai tarin 'yan Nijar mazauna kasashen ketare da za su iya samun damar yin zabeHoto: Marou I. Madougou/DW

Tuni ma dai ta soma aikewa da kayan aiki zuwa kasashen da za a yi kidayar, inda aka amince da tsarin irin ma'aikatan da ya kamata a dauka. A cewar Malam Nassirou Seidou shugaban kungiyar farar hula ta Muryar Talaka a Jamhuriyar Nijar din, ya kyautu a a wannan karo a nuna kwarewa cikin aikin kidayar. Kasahse 15 dai da za a yi wannan kidaya a cikinsu, sun hadar da Aljeriya da Jamhuriyar Benin da Burkina Faso da Kamaru da Cote d'Ivoir da Ghana da Mali da Najeriya da Maroko da Senegal da Chadi da Togo da Beljiyam da Faransa da kuma Amirka. Za dai a kwashe tsahon makonni biyu ana gudanar da aikin kidayar a kowace kasa, inda za a fara daga ranar 15 ga watan Oktoba mai zuwa.