Nijar: Mutane miliyan 3 na bukatar agaji
February 19, 2020Talla
A wani rahoton Asusun kula da yara ta Majalisar wato Unicef ta bakin Felicite Tchibindat, wakiliyar Unicef a yankin ta ce, jama'a na cikin yanayi na bukatar taimako a yayin da suke fuskantar barazanar tsaro daga masu tayar da kayar baya. Amma sun rungumi kaddara duk da matsin da suke ciki inji wakiliyar wanda ta ce abin koyi ne ga sauran kasashen duniya.
Sanarwar na zuwa ne bayan wani iftala'i a ranar Litinin din da ta gabata, inda mata da yara akalla 20 suka mutu a sakamakon wani turmutsitsi a wani sansani da ake rabon abinci da kudi wa 'yan gudun hijira.