Nijar na cikin ruɗanin siyasa
November 20, 2013 A jamhuriyar Nijar ƙawancan jam'iyyun da ke yin mulki na MRN ya fitar
da sanarwa. Inda ya mayar da martani a kan jerin wasu zarge-zarge da ƙawancan jam'iyyun adawa na ARDR ya yi wa shugaban ƙasar ta Nijar da gwamnatinsa a cikin wata sanarwa da su ka fitar a makon da ya gabata. Haka zalika ƙawancen jam'iyyun da ke milkin ya bayyan gamsuwarsa da rinjayen da ya samu a mahawarar gwada farin jinin gwamnati da aka gudanar a majalisar dokokin ƙasar a cikin watan jiya
Ɗaya daga cikin batutuwan da ƙawancen jam'iyyun da ke mulkin ƙasar ta
Nijar na MRN ya mayar da martani a kansa a cikin sanarwa ta sa, shi ne na
zargin sakaci da 'yan adawar su ka ce gwamnatin ta yi dangane da
haɗarin mutuwar yan Nijar 92 a cikin sahara yau da yan makonni. Dokta
Sagir shugaban jam'iyyar PDP Bushara, shi ne Kakakin wanann sanarwa ta ƙawancan jam'iyyun da ke mulkin na MRN.
Haka zalika a cikin sanarwar da ƙawancen jam'iyyun adawar na ARDR ya yi
a baya, ya zargi shugaban ƙasar da nuna ƙabilanci dama ɓangaranci a
cikin tafiyar da mulkinsa. Suna masu ba da misali da wani karin magana
na ɗan ƙaramin gatarinka ya fi sari ka bani. Su ka ce shugaban ƙasar
ya ce lokacin wani taro da ya gudanar a cikin jiharsa ta aihuwa ta
Tawa. Dangane da wanannan zargin da jam'iyyun masu mulki na MRN
ya mayar da martani yana mai cewa.
Daga ƙarshe dai ƙawancan jam'iyyun da ke mulkin ya sake jaddada goyon
bayansa ga shugaban ƙasa da gwamnati sa tare da sake sanya kira ga 'yan adawa masu ra'ayin kishin ƙasa, da su zo su kawo wa gwamnatin goyon bayansu domin gina ƙasa
Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Usman Shehu Usman