1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar na fiskantar matsalolin tsaro

September 20, 2013

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta mayar da martani kan rahoton da ya bayyana cewa, kasar na fiskantar barazanar tsaro daga kasashe makwabta.

This photo taken on June 1, 2013, shows soldiers standing guard at the entrance of the main prison in Niamey. Inmates in Niamey's main prison killed two guards on June 1, officials said, a week after twin suicide bombings claimed 20 lives in the west African country. Three inmates charged with terrorist offences tried to had break out of the prison, prosecutor Ibrahim Wazir Moussa said on state television. AFP PHOTO / STRINGER (Photo credit should read STR/AFP/Getty Images)
Jami'an tsaron Nijar, bayan wani harin a gidan yarin YamaiHoto: STR/AFP/Getty Images

Cikin wani rahoto na baya-bayan nan da ta fitar, kungiyar kare afkuwar rikice-rikice mai suna Crisis Group ta bayyana cewa, sanadiyyar tabarbarewar tsaro a yankunan Janhuriyyar Nijar, ya sanya gwamnatin kasar bayar da fifikon kashe kudade ta fuskar tsaro fiye da sauran fannonin ci gaban rayuwa.

Crisis Group ta bayar da misali da tagwayen hare-haren da aka kai a birnin Agadez da wanda aka kai ma'aikatar hako ma'adinan yuraniun dake yankin Arlit cikin watan Mayu. Har ila yau da wanda aka kai kan gidan yarin kasar da ke birnin Yamai a ranar daya ga watan Yuni, al'amarin da manazarta da su ka hadar da Ibrahim Bah na kungiyar Crisis Group ke ganin hakan ya bayyana karara irin barazanar tsaro da kasar ke fuskanta.

Mahamadou Issoufou, shugaban kasar NijarHoto: N. Colombant

A cewar kungiyar barazanar dai na zuwa ne daga makobtan kasashe da suka hadar da arewacin Mali mai fama da kungiyoyin jahadi, da Boko Haram a arewacin Najeria, da ke tsallakowa domin tserewa harin dakarun Najeriyar. Ibrahim Bah yace wanann barazanar kadai ta ishi jefa Nijar cikin fargabar shiga tsakiyar kungiyoyin 'yan ta'adda.

Da yake mayar da martani akan wannan rahoto, ministan sadarwa Jamhuriyar Nijar Malam Yahouza Sadissou, yace hare-haren da aka samu a wasu yankunan Nijar baya nufin gwamnati ta yi sako-sako ga matsalar tsaro.

Yahouza Sadissou, ministan sadarwan kasar NijarHoto: DW

Ministan ya ce, dukkanin matakan da ake dauka ba za ka ce ka samu nasara dari bisa dari ba, abin da ya faru a Agadez da birnin Yamai bai taka kara ya karya ba, in da an kwatanta da tashe-tashen hankulan da kasashe makwabta ke fama da shi. Babban abin da gwamanti ta sa a gaba shi ne na ganin ta kare al'ummarta, ba zai hana a samu wani rikici da bai taka kara ya karya ba.

Kungiyar ta Crisis Group, ta kuma yi tsokaci game da yadda gwamnatin Nijar ta ba da wani fifiko wajen kashe kasafin kudin kasar ga tsaro, fiye da sauren fanonin ci-gaban rayuwar al'umma. Matakin da Mininstan sadarwa Yahouza Sadissou ke cewa, dole ne a yi wa demokradiyyar kasar uzuri, tun da ta na kan tafarkin koyo ne ba waa wani kwari ta yi ba.

Yanayin noma a wasu yankunan kasar NijarHoto: Fatoumata Diabate/Oxfam

Har ila yau rahoton kungiyar kare afkuwar rikice-rikice, ya ce yanayin siyasar da ake ciki da ya baiwa gwamnatin neman hadin gwiwar jamiyyun adawa domin kafa gwamnatin hadin kai, ba komai ya ke nunawa ba illa bayyanar kamari da matasalar kasar ta yi. Akan wannan ma dai ministan Sadarwa ya danganta rikice rikicen na siyasa da abin da demokaradiyya ta gada.

A karshen wannan rahoto kungiyar ta Crisis Group ta yi kira ga shugaban Jamhuriyar ta Nijar, Mouhamadou Issoufou da ya matsa kaimi, domin cika alkawuran da ya daukar wa talakawa.

Mawallafi: Youssoufou Abdoulaye

Edita: Usman Shehu Usman