Nijar: Riciki a majalisa kan batun cin hanci
April 21, 2017Tun a ranar 17 ga watan Maris na wannan shekarar ne majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar ta kafa wani kwamiti mai kunshe da mambobi 12 daga ciki wakilan 'yan adawa wanda majalisar ta umarce su da su gudanar da kwakwaran bincike kan badakalar CFA miliyan dubu 200 da ake zargin Malam Hassoumi Massaoudou wanda a wancan lokaci ya ke a fadar shugaban kasa ya karkata akalarsu ya zuwa wani asusun ajiya da ke kasar Dubai. Soumana Sanda dan majalisar dokoki na bangaren adawa kuma mataimakin shugaban kwamitin binciken da majalisar ta kafa ya ce ba da saninsu ba aka ajiye rahoton:
"Yau da safe kawai muna cikin majalisa sai shugaban majalisa ya ce an ajiye rahoton binciken 'yan majalisa, mun ce wannan abun mamaki ne kuma mun gayawa mutane da cewar an ajiye rahoton ba tare da saninmu ba kuma wannan ya nuna kenan da cewar akwai alamar boyewa mutane gaskiya kuma ya tabbatar da cewar daman ba don a tabbatar da gaskiya ba ne ya sa aka kafa wannan kwamitin ba."
'Yan adawar dai na kokawa ne da yin riga malam masallaci daga bangaren masu rinjaye da ma rashin basu da wadatacen lokaci don gudanar da binciken duba da rashin yawansu a cikin kwamitin kana kuma bangaren na masu mulkin ya yi gaba-gadin ne ba tare da shawartar su ba. Sai dai da ya ke mayar da martani shugaban kwamitin binciken Honorable Saddi Soumaila na jam'iyyar PNDS Tarayya ya ce batun ba haka ya ke ba:
"Kwanaki 10 mukayi muna wannan rubutu, mun ce su zo suka ki, ni kaina na kirasu na kuma kira mataimakin shugaban kwamitin nan ya zo ya ki ya ya zo ya kashe wayarsa, ni kuma ni ne shugaban kwamitin kuma ni nake sa hannu. To sai dai abin tambaya shi ne yanda ku ka dauki dan takaitacen lokaci game da wannan abin duba da yanda kudin ke da makudan yawa ne fa kunyi binciken ko cikin kwanaki goma kawai ?"
Wannan lamarin na zuwa ne ya yin da hankalin 'yan kasar ya karkata bisa irin sakamakon da gungun 'yan majalisar za su fitar dangance da badakalar ta makudan kudin duba da yanda maganar kudin ta kai ga bangarorin biyu na adawa da masu mulki yin mai abu ya rantse marar abun shi ma ya rantse.