1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Rishin bada hadin kai kan harkar tsaro

Salissou Boukari
October 23, 2017

Kwamitin tsaro na majalisar dokokin Nijar ya nuna damuwa kan rashin bayar da hadin kai ga jami'an tsaro da ke fagen daga masu yakar ayyukan ta'addanci, inda ya ce mazauna kauyuka ba su taimakawa.

Niger Soldaten
Sojojin Nijar masu sintiriHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Batun na kin bayar da hadin kai da bayannan sirri daga al'ummar kasar fararen hulla mazauna yankunan da ake fama masu ayyukan 'yan ta'adda, ya sake bijirowa ne biyo bayan karuwar kai hare-haren ta'addanci a wasu iyakokin kasar ta Jamhuriyar Nijar da kasashe masu fama da yan ta'adda wanda kuma sakamakon hakan ya yi sanadiyar hallaka jami'an tsaron kasar dama. Lamarin da kwamitin kula da tsaro na majalisar dokokin ta Nijar ya nuna tsananin damuwar sa dangance da salon da matsalar ta ke ci gaba da dauka musamman ma a yammacin kasar. Honorable Hama Assah shi ne shugaban kwamitin tsaron na majalisar dokoki:

Yunkirin samar da tsaro a iyakokin Nijar

inistar Tsaron kasar JamusUrsula von der Leyen, tare da Ministan cikin gida na Nijar Bazoum MohamedHoto: picture-alliance/dpa/B. Pedersen

"Ba wai bamu cewa ba su bada hadin kai ne ba akwai wasu abubuwan da idan mutun ya gansu yasan cewa akwai lauje cikin nadi wanda kamata ya yi idan kaga wani dan ta'adda ko bakon sani cikin mota ko bisa babur kaga baka kira wani dan doka ko wani wanda ke iya kai labari ba ka bashi labarin ba, hakan bai dace ba. Sai kawai su yi shiru." 

To amma sai dai wani abin da ke ci gaba da daure wa wasu masu sharhi kai, shi ne irin yanda a cikin dan takaitacen lokaci gwamnatin ta Nijar ta yi hasarar dimbin sojojinta da ke fagen daga bisa wani abin da wasun suka kira rashin samun tallafi na cikakkun bayannanai daga talakawan yankin da ake fama da tashe-tashen hankula,  ko da yake a cewar Malam Laouali Abdoubakar na kungiyoyin farar hulla matsalar ba wai ta rashin hadin kan talakkawan yankin ba ce kawai:

"Wasu lokuttan mazauna garuruwan na da tsoro saboda suna gudun fadi gidan wane ne bakon ke zuwa wani abu ya faru kenan kana ta kanta hakan kuma akwai cewar jami'an tsaro su rinka yi su na shiga irin ta jama'a don samun hadin kai domin wasu lokutan kayan su tsoro suke bai wa mutanen karkara."

Sabuwar mahawara kan hare-hare

Jirgi maras matuki na sojojin Faransa a NijarHoto: Getty Images/AFP/P. Guyot

Yawaitar kai hare-haren ta'addancin dai da ya yi sanadiyar mutuwar sojojin kasar ta Nijar da dama ya kuma sake tayar da mahawarakan batun kasancewar sojojin kasshen waje da ke zaune a kasar ta Nijar. Wannan lamarin na kokawa kan rashin samar da bayyanan sirri ga jami'an tsaro na zuwa ne a ya yin da wasu rahotanni ke cewar hukumomin tsaro sun cafke hakimin wani kauyen Tongo Tongo cikin jihar Tillabery, inda a ke zarginsa da gama baki da 'yan ta'adda biyo bayan harin da ya hallaka wasu sojojojin na Nijar da na Amirka a farkon wannan watan na Octoba.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani