1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Harkokin kudi a cikin bankuna na shirin daidaita

Salissou Boukari AH
February 28, 2024

Cire takunkumi ECOWAS da UEMOA a kan Nijar zai sake bai wa kasar ragamar tafiyar da harkokin kudi a cikin bankuna wajen cirar kudade bayan da aka shafe watanni shida na tsaiko.

Hoto: SEYLLOU/AFP

A cikin wata wasika da babban Darektan bankin yammacin Afirka na  reshen  Nijar ya fitar zuwa ga manyan Darektocin bankuna dabam-dabam na kasar ta Nijar, ya ce su na masu farin cikin mika wa daraktocin sanarwar karshe na babban taron gaggawa na shugabannin kasashe da gwamnatoci na kungiyar kasashen yammacin Afirka masu amfani da kudadan CFA ta   UEMOA, wanda ya gudanar a ranar 24 ga Fabrairu a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya. Inda babban daraktan na BCEAO reshen Nijar ya kara da cewa, za su yi godiyya ga matakan da bankuna za su dauka don ganin an aiwatar da hukunce-hukuncen da babban zaman taron ya dauka domin hukunci ne da ta kamata a aiwatar da shi nan take. Sai dai har ya zuwa yanzu masu zuwa bankuna sun ce da sauran zomo a kaba. Alhaji Baba El-Makiyya shugaban kungiyar farar hula mai kula da kare hakin jama'a ya ce ya kyautu a gaggauta aiwatar da wannan mataki.

Har yanzu dai akwai tsaiko wajen cire kudade a cikin bankuna

Hoto: Michael Weber/IMAGEPOWER/IMAGO

A fuskar kananan 'yan kasuwa da suka dandana kudarsu wajen samun kudadansu a bankunan ta bakin Adamou Isma'ila, yana ganin yadda suka jure tsawon watanni bakwai suna fuskantar kalubale ta dalilin matakin ECOWAS da UEMOWA, za su jure na 'yan kwanaki domin ganin komai ya daidaita wajen samun kudade yadda ake bukata a cikin bankuna.

Jami'an bankunan sun ce har 'yanzu ba  su samu kudade ba daga babban banki na BCEAO

Hoto: Million Hailesillasie/DW

Yayin da na tuntubi wani babban jami'in  banki da bai so na nadi muryarsa ba, ya ce lamarin gare su yana da dan sarkakakiya, domin kuwa ya ce suma suna zaman jira ne babban bankin na BCEAO ya tabbatar musu cewa ya samu kudadan da zai rarraba wa bankunan na cikin kasar ganin cewa watannin da aka dauka babban bankin ya na bukatar samun kudadan amma kuma ba su da tabbacin ko an samu adadin kudadan da ake bukata domin bankunan kasar cewa lamari ne da sai an bi shi sannu a hankali kafin komai yake   zuwa daidai.