1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Nijar: Shekara guda bayan juyin mulkin soji

Abdullahi Tanko Bala
July 26, 2024

Shekara guda da juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhhuriyar Nijar, har yanzu batun tsaro na ci gaba da haifar da cece-kuce.

Shugaban mulkin sojin NIjar, Janar Abdourahamane Tiani
Shugaban mulkin sojin NIjar, Janar Abdourahamane TianiHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

Shugaban mulkin sojin Abdourahamane Tiani a jawabin da ya yi wa 'yyan kasar ya ce kasar ta yammacin Afirka ta kama hanyar zama mai 'yancin cin gashin kanta tare da shawo kan kalubalen da suka dabaibaye ta a fannoni dfa dama.

Tun bayan juyin mulkin na ranar 26 ga watan Julin 2023, kasar ta fara nesanta kanta daga uwargijiyarta Faransa wadda ta yi mata mulkin mallaka ta kuma karkata zuwa ga sabuwar kawa wato Rasha.

A waje daya kuma dangantaka tsakanin NIjar da makwabciyarta Jamhuriyar Benin ta yi tsami da har ya lalata huldar diflomasiyya a tsakaninsu da ma shafar harkokin tattalin arzikin kasashen biyu, lamarinn da ya kai Nijar ga rufe muhimmin bututunta na mai zuwa Benin.

Yayin da dangantakar ta tabarbare shugabannin kasashen Afirka yamma ECOWAS na shirin tattauina takaddamar taron yankin da za su yi a nan gaba.

Ko da yake kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso da suka yi juyin mulki sun fice daga kungiyar ECOWAS tare da kafa wata sabuwar kungiyar kawance a tsakaninsu maana na ganin rarrabuwar kawuna ba za ta amfana komai ba, hadin kai da fahimtar juna da kuma yin aiki tare shi ne zai kawo cigaba ga yankin da al'umarta baki daya.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani