1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara guda da juyin mulkin Nijar

Gazali Abdou Tasawa LMJ
July 24, 2024

A daidai lokacin da ake cika shekara guda da juyin mulkin da sojojin Nijar karkashin jagorancin Janar Abdourahmane Tiani suka yi, ana ci ga da fuskantar matsalar tsaro da ke zama babbar hujjar sojojin ta kwatar mulki.

Nijar | Yamai | Juyin Mulki | Sojoji | Janar Abdourahamane Tiani
Jagoran gwamnatin juyin mulkin Jamhuriyar Nijar Janar Abdourahmane TianiHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP

Tabarbarewar harkokin tsaro sakamakon hare-haren 'yan ta'adda na sahun gaban dalilan da sojojin Jamhuriyar ta Nijar karkashin jagorancin Janar Abdourahmane Tiani suka bayyana, a matsayin hujjarsu ta kifar da tsababbiyar gwamnati Shugaba Mohamed Bazoum. Tun daga wancen lokacin hukumomin tsaron kasar sun sha ikirarin daukar matakan kara yawan jami'an tsaro da samar musu da kayan aiki a yankunan da ke fama da matsalar, a jihohin Diffa da Tahou da Maradi da Agadez da kuma Tillabery da matsalar ta fi kamari. Sai dai da yake tsokaci kan wannan batu, Malam Amadou Harouna Maiga shugaban kungiyar fafutukar kare hakkin al'ummar jihar Tillabery ya ce ko da yake sojojin sun iya nasu kokarin amma dai akwai sauran rina a kaba.
Sai dai wasu masana harkokin tsaro a Nijar din kamar Malam Abbas Abdoulmoumouni na ganin an samu gagarumin ci gaba a fannin tsaro a tsawon wannan shekara, musamman ganin yadda kasar ta fito daga kangin takunkumin tattalin arzikin da aka kakaba mata. To amma Malam Moussa Mounmouni mai bai wa Shugaba Bazoum da sojojin suka kifar shawara a fannin harkokin tsaro a lokacin mulkinsa ya ce, Nijar ta fuskanci koma-baya sosai idan aka kwatanta da lokacin hambararriyar gwamnatinsu. A cewarsa a fannin tsaro kwata-kwata harakokin sun kara lalacewa, domin daga ranar 26 ga watan Yulin 2023 an rasa jami'an tsaro sama da 780 a filin daga. Babu dai wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da wadannan alkaluma da wannan mashawarci na hambararren shugaban kasar ya bayar, amma kuma har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton gwamnatin juyin mulkin Nijar din ba ta fitar da nata alkaluman adadin sojoji da fararen hular da suka halaka a tsawon mulkin nasu na shekara guda.

Sojojin Nijar na daga cikin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon rashin tsaroHoto: DW/S. Boukari

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani