1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Nijar: Shirin mayar da almajirai garuruwansu

Gazali Abdou Tasawa
August 16, 2024

A Jamhuriyar Nijar hukumomin birnin Yamai sun kaddamar da wani shiri na kamen mabarata da iza keyarsu zuwa garuruwansu na asali bayan yi masu rijista.

Bettelnde Kinder in Dutse, Nigeria
Hoto: DW/Z. Rabo Ringim

Mahukuntan sun dauki wannan mataki ne a wani yunkurin neman kawo karshen yaduwar mabarata a birnin Yamai musamman a wannan lokaci na damina. Mahukuntan birnin sun kuma sha alwashin duk wanda aka mayar da su suka dawo, to za a aika su zuwa gonakin gwamnati domin su yi aikin karfi. 

Mahukuntan sun dauri aniyar kawo karshen wannan dabi'a ta bara wacce suka ce na neman zama tamkar wata annoba a birnin. A kan haka ne suka dauki matakin kamen mabaratan da kuma iza keyarsu zuwa garuruwansu na asali da ma yin barazanar hukunta duk wadanda za su  sake dawowa a cikin birnin bayan mayar da su garuruwan nasu. Malam Ibrahim Toudou babban kwamishinan ‘yan sanda da ke jagorancin tafiyar da kamen ya yi karin baynai kan matakin

Hoto: DW/A.M. Waziri

"Almajirai masu yin bara wannan ya zame wa Nijar kamar gyambo. In kuka duba cikin garin Yamai, yara da manya mafiyawancinsu lafiyarsu lau, amma su zo suna sana'ar bara wacce ba ta kawo alkhairi cikin kasa. Lallai in mutum miskini ne ana iya taimaka masa, to kowa ai ya san miskini. To yanzu dai an ba mu umurni, wadannan mutane a kwashe su a mayar da su garuruwansu"

Yanzu haka dai tuni ‘yan sanda a cikin motoci suka fara sintiri a cikin birnin suna tattara almajiran domin aika su garuruwansu. Matakin da Alhaji Salissou Amadou wani dan fafutika ya ce ya yi daidai.

Hoto: DW/A.M. Waziri

"Ana cikin damuna ya kamata mutanen karkara su tsaya su yi noma musamman ganin cewa damunar bana ta na tafiya da kyau. Kamata ya yi su tsaya su ga yadda Allah yayi da sakamakon damanar. Idan ba a samu yadda ake so ba, nan ana iya fita. Amma bai kamata ba mutane su mayar da bara sana'a. Idan maganar yunwa ce, yau Allah ya sa albarka a damuna yanzu babu yunwa. Dan haka ina ganin matakin da muhukunta suka dauka ya yi daidai”

To sai dai wasu masu fafutikar kare hakin dan Adam na ganin akwai bukatar mahukuntan birnin na Yamai su yi taka tsan-tsan wajen aiwatar da wannan shiri nasu domin kauce wa shiga hakin mabaratan: Malam Soule Oumarou na kungiyar FCR na daga cikin masu nuna wannan damuwa.

Hoto: DW/Z. Rabo Ringim

”Wannan lamari ya kamata a yi taka tsan-tsan saboda a gaskiya akwai wadanda lamarin ya kamasu dole saboka yunwa da fatara. Kenan idan an kama su an kai su garuruwansu wani bai da gonar wani kuma ba shi da abin noman. Kenan ya kamata a yi masu tanadi abin da za su ci ko kuma wanda za su yi wata sana'a. Dan ba shakka akwai wadanda ko an mayar da su za su dawo. An ce za a kama su a kai su gona su yi aikin karfi. To nan ma akwai bukatar yin taka tsan-tsan domin suna da hakki. Wanda aka kama aka kai yin aiki a cikin gonakin to ya kamata a ce in sun yi aiki za su samu wani amfani""

Hukumomin birnin na Yamai dai sun sanar da cewa za su yi rijistar mabaratan da kuma daukar hoton yatsunsu da ma hotonsu irin yadda ake yi wa wadanda aka samu da aikata laifi a gaban hukuma kafin aika su zuwa garuruwan nasu ta yadda duk wanda ya sake dawowa birnin aka kama shi zai hadu da fushin hukuma.