1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan ta'adda sun sake kai hari a Nijar

Gazali Abdou Tasawa AH
July 12, 2021

A Nijar sojojin gwamnati sun hallaka mayakan 'yan ta’adda kimanin 40 da karbe kayan yaki masu yawa a lokacin wani dauki ba dadi da suka ka yi da tsagerun a wani hari da suka kawo a kauyen Chomabangou na Jihar Tillabery.

Niger Agadez Armee Soldaten
Hoto: picture-alliance/Zuma/A. Fox Echols Iii

Sanarwar da ofishin ministan tsaro na kasar Nijar ya fitar ta nunar da cewa 'yan ta’adda a saman baburra dauke da manyan makamai daga makobciyar kasar Mali suka kai hari a kauyen Chomabangou inda dama suka taba hallaka fararan hula kimanin 100 a watanni uku da suka gabata. Sanarwar ta ce sai dai a wannan karon ‚yan ta’addar sun kwashi kashinsu a hannu a sakamakon martanin da sojojin kasar ta Nijar na Operation Almahaou wato Guguwa suka mayar masu inda suka hallaka akalla ‚yan ta’adda 40 suka kuma kwace baburra 14 da tarin makaman yaki da suka hada da manyan bindigogi masu jigida. Da yake tsokaci kann wannan nasara Honnorable Kalla Moutari dan majalisar dokoki daga jam’iyya mai mulki ta PNDS Tarayya kana tsohon ministan tsaro,jinjinawa sojojin kasar ya yi da kuma barka ga al’ummar yankin na Tillabery.

'Yan ta'addar sun kashe sojojin gwamnati guda hudu

Hoto: Facebook/Präsidentschaft Tschad

Sojojin Nijar hudu suka yi shahada a filin dagga da wasu fararan hula biyar a yayin da wasu sojojin uku suka jikkata. Sai dai Malam Nasirou Seidou na kungiyar muryar talaka a Nijar ya ce nasarar da sojojin Nijar ke samu a yanzu abin alfahari ce amma zai fi kyau a dauki matakan hana wa ‚yan ta’addar iya kawo farmakin baki daya. Gwamnatin Nijar din dai na kara karfafa matakan tsaro a yankin na Tillabery na kan iyaka da Mali a daidai lokacin da yanzu haka wata zazzafar tankiya ta barke a kwanakin nan tsakanin 'yan Nijar da 'yan Mali wadanda suka soki lamirin shugaban Nijar a game da kalaman da ya yi a Faransa inda ya zargi sojojin Mali da kwarewa wajen iya juyin mulki amma ba tare da iya yin wani katabus ba a fagen daggar yaki da ‚yan ta’adda.