Nijar ta ce ba dimukuradiyyar waje take so ba
October 6, 2025
Shugaban gwamnatin mulkin sojan a Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahmane Tiani ya bayyana aniyarsa ta mayar da hankali ga tabbatar da tsaro da zaman lafiya a kasar a maimakon gaggauta mayar da kasar kan turbar dimukuradiyya. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu labaran da ake yadawa a shafukan sada zumunta a kasar a baya bayan nan, ke cewa akwai babbar barka a tsakanin mambobin majalisar ceton kasa ta sojojin ta CNSP, kan batun shirya zabe da komawa mulkin dimukuradiyya a kasar.
Wasu labarai da suka yi ta yawo a shafukan sada zumunta a kasar ta Nijar a kawanakin baya bayan nan ne dai suka nunar da cewa majalisar ceton kasa ta sojojin Nijar ta CNSP ta gudanar da wani zaman na tattauna yiwuwar mayar da kasar kan turbar dimukuradiyya.
Zaman da a lokacinsa ministan tsaro na kasa da takwaransa na cikin gida suka nuna adawarsu a bayyane game da duk wani shiri na mayar da kasar tafarkin dimukuradiyya. To sai dai a jawabin da ya gabatar a ziyarar da ya kai a jihar tillabery a karshen mako, Shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar ta Nijar, shugaban kasa Janar Abdourahmane Tiani ya ce wannan batu zuki ta malle ce, hasalima ya ce labarin na gudana ne a karkashin wani shiri da Faransa ta kitsa na amfani da shafukan sada zumunta na zamani wajen yada a kai a kai labaran karya da shaci fadi wadanda za su ruruta wutar rikici da haddasa rudani a tsakanin al'umma a cikin kasashen AES na Nijar Mali da Burkina Faso. Kuma ya ce batun mayar da Nijar a tafarkin dimukuradiyya irin wacce kasashen Turawa suke nufi, sam bai taso ba.
''Ya ce wai wace irin dimukuradiyya ma ce ake batu? Domin mu a wurinmu, dimukuradiyyarmu na nufin tsira da rayukanmu, tsira da mutuncinmu, samar wa kasarmu cikakken ‘yancin kanta. Kuma al'ummar Nijar ce kadai ke da hurumin shata hanyoyin da za mu bi domin cimma wadannan bururruka namu ba wai wata babbar kasa ba ta ketare.''
Wadannan kamalai na Shugaba Tiani kan batun dimukuradiyya na zuwa ne a daidai lokacin da kuma a watanni baya bayan nan ake ta rade-radin cewa yana shirye-shiryen shirya zabe a shekara ta 2026 domin mayar da mulki ga farar hula.
Sai dai Malam Mohamed El Kebir na Kawancen kungiyoyin farar hula na Synergie ya ce suna goyon bayan ra'ayin shugaban kasa game da batun kin gaggauta mayar da kasar kan turbar dimukuradiyya.
Amma kuma Malam Sahanin Mahamadou wani mai adawa da mulkin soja a Nijar, ya ce bai yi mamaki ba a game da adawar gwamnatin mulkin sojan ta mika mulki ga farar hula.
A jawabin nasa dai, Shugaba Tianiya yi kashedi ga wasu ‘yan Nijar da yake suke ciki kasa suna ci gaba da hada kai da Faransa wajen cuta wa Nijar, su gaggauta barin kasar su koma Faransa domin ba su da wajen zama a kasar Nijar.