An dage dokar hana noman tattasai da kamun kifi a Diffa
March 7, 2019Gwamnatin kasar Nijar ta kakaba dokar hana kasuwancin ne shekaru hudu da suka wuce, bisa zargin kudaden da ake samarwa daga sana'ar na tallafa wa mayakan kungiyar Boko Haram, inda suke karbar kudaden lanho ga masu sana'ar, lamarin da ya jefa al'ummar yankin DIffa a cikin fatara da talauci.
Rahotanni sun ce ko baya ga halarta kamun kifi da noman tattasai, gwamnatin Nijar ta ba da wani kwarya-kwaryan 'yanci na sayar da man fetur da takin zamani, bisa hujjar samun cikakken tsaro a yankin, wadanda dukkansu a can baya hukumomin suka zargi Boko Haram na amfani da su wajen samun kudaden shiga da ke sa suna kara zafafa hare-hare a yankin.
Tun a shekarar 2015 ne kungiyar ta masu ikirarin jihadi ta fara kaddamar da hare-hare a Nijar tare da yin sanadi na mutuwar mutane da dama.