1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta dakatar da bayar da lasisin hakar ma'adanai

January 25, 2024

Majalisar gwamnatin mulkin soji a Jamhuriyar Nijar ta dakatar da bayar da sabbin lasisin hakar ma'adanai tare da bukatar a zurfafa bincike a fannin.

Kamfanin Orano mallakin Faransa da ke aikin Uranium a Nijar
Kamfanin Orano mallakin Faransa da ke aikin Uranium a NijarHoto: Maurice Ascani/Areva/AP Photo/picture alliance

A cewar ma'aikatar kula da harkokin ma'adanai ta kasar, dakatar da bayar da lasisin mataki ne na wucin gadi.

Kafin nan dai, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa ma'aikatar kula da hakar ma'adanai ta Nijar din ba ta sanar da dalilin dakatarwar ba a cikin sanarwar da ta fitar a ranar 22 ga watan Janairun 2024.

Karin bayani: Kalubalen aikin hakar uranium a Nijar

Kasar Nijar ita ce kasa mafi samar da sinadarin Uranium a nahiyar Afirka, kana ta bakwai a duniya.

Masu aikin hakar zinari da dama ne dai suke aikin hakar ma'adanai a kasar.