1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Nijar ta dakatar da tunkuda man fetur dinta zuwa Benin

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 14, 2024

Ministan man fetur din kasar Mahamane Moustapha Barke ne ya sanar da hakan, lokacin da ya ziyarci cibiyar tunkudo danyen man

Hoto: Boureima Hama/AFP/Getty Images

Jamhuriyar Nijar ta sanar da dakatar da tunkuda danyen man fetur dinta cikin bututun da ke zuwa Jamhuriyar Benin, sakamakon takun saka da rikicin diflomasiyya da ke kara zafi tsakanin makwabtan kasashen biyu.

Karin bayani:Rikici ya ki cinyewa tsakanin Talon da Janar Tiani

Ministan man fetur din kasar Mahamane Moustapha Barke ne ya sanar da hakan, lokacin da ya ziyarci cibiyar tunkudo danyen man, don cika umarnin shugaban mulkin sojin kasar Janar Abdourahmane Tiani na rufe ta.

karin bayani:Nijar ta sanar da dakatar da tura danyen man fetur dinta zuwa Benin

A makon da ya gabata ne dai hukumomin Jamhuriyar Benin suka kama jami'an kamfanin man fetur din Nijar guda biyar, inda suka zargi biyu daga cikinsu da cewa 'yan leken asirin gwamnatin sojin Nijar din ne, amma suka yi badda bami a matsayin ma'aikatan kamfanin man fetur din WAPCO na Chaina.