Nijar ta fada cikin rudanin siyasa
August 25, 2015 A yayin da ita jam'iyar CDS Rahama ta shiga sabuwar takaddama bisa rikicin jagoranci, wani sabo shi ne sanarwar da firaminista jamhuriyar ta Nijar, ya aika wa Mahamane Ousman, wasikar cewa idan za'a yi zaman taron majalisar sasanta rikicin siyasa wato CNDP bangaren sa, baya da kujera a taron, sai dai bangaren Abdou Labo. Tuni dai bangaren Ousman ya ta tashi bisa mumman martani kan cewa matakin na gwamnatin Nijar ya sabawa doka, tunda har yanzu akwai sauran shari'a kan takaddamar shugabancin jam'iyar ta su wanda ke gaban kotu.
A wani abu da ke nuna yadda 'yan adawa ke cewa gwamnatin shugaba Mahamadou Issoufou ke kuntata musu, an kama wani dan majalisar dokoki bangaren adawa. Lamarin ya faru ne daidai lokacin da rahotani suka tabbatar da yanzu haka jami'an tsaron kasar na ci-gaba da tsare wani dan majalisar dokoki na bangaren adawa daga jam'iyar Moden-Lumana Afrika ta tsohon kakakin majalisar dokokin kasar Hama Amadu, kamun da ke zaman wata bita da kullin siyasa a cewar 'yan adawan:
Da yammacin wannan Litinin 24.08.2015 ne dai jami'an tsaro a birnin Kwanni da ke jihar Tahoua su ka cafke dan majalisar dokokin honnorable Ahmed Babaty bisa zargin da aka yi masa na cewa wai ya rushe igiyar da jam'ian tsaro suka gitta kan hanya, don binciken ababen hawa, kusa da kawyen Abalak da ke jihar Tahoua kamar yadda Hamza Inda, shugaban hadin gwiwar jam'iyun adawa na ARDR a jihar ta Tahoua ya tabbatarwa tashar DW a ta wayar tarho:
Amma fa a gefe guda ita jamiyar PNDS Tarayya da ke mulki, ta sami rarrabuwar kawuna, musamman tsakanin matasa da a yanzu haka taurarunsu ke tashi fiye da na tsoffin kuraye a jam'iyar. Wannan kuwa ya tabbatar yadda Jamhuriyar Nijar ke kara fadawa cikin rudanin siyasa gabanin zabukan kasar da ke tafe.