Nijar ta farfado da horon soja ga masu yi wa kasa hidima
October 29, 2024Tun shekaru 32 ne hukumomin kasar Nijar suka dakatar da bayar da horon aikin soji ga masu yi wa kasa hidima ko kuma civicars a Faransance, duk da cewa doka ta tanadin bayar da wannan horo a tsawon kwanaki 45 a karshen aikin hidimar kasar na tsawon shekaru biyu. Sai dai gwamnatin mulkin soja ta sake farfado da wannan fanni a karkashin gyaran fuskar da suka yi wa dokar ta tsarin aikin masu yi wa kasa hidima.
Ya ya masu yi wa kasa hidima suka karbi garambawul?
Tsayyabou Ali Oumourana da ke zama sakataren hulda da jama’a na kungiyar masu yi wa kasa hidima yana goyon bayan farfado da horon soji, inda ya ce: " Mun tattauna da ministan ilimi mai zurfi, inda ya kwatanta mana cewa abin da ya sa aka sa wannan horo domin a aikin horan soja, ana koya masu kishin kasa da son kasa da yadda mutum zai kare kasa... Lokacin da aka yi juyin mulki, an yi ta yi wa kasa barazanar kawo mata hari. Da duk masu aikin yi wa kasa hidima sun yi wannan horo na soja, da sun taimaka wajen kare kasa."
Karin bayani: Kaddamar da makarantar horon soja a Nijar
Ita ma majalisar matasa ta kasa ta Conseil National de la Jeunesse ta bakin shugabanta Sidi Mohamed cewa ta yi matakin ya yi daidai, ta la’akari da jerin matsalolin tsaro da ke barazana ga kasar Nijar. Ya ce: "Matakin abu ne mai mahimmanci musamman ganin cewar kasarmu na fama da matsaloli da dama na tsaro, na ta’addanci da tsageru masu tayar da zaune tsaye ga kasa. Duk wannan idan aka bai wa matasa horon soji, za su taimaka wajen tsare kasarmu."
Shawarar da masu yi wa kasa hidima suka bayar
Jami’o’in kasar Nijar na a sahun gaban wajen samar da masu yi wa kasar hidima. Saboda haka ne kungiyar daliban jami’ar birnin Yamai UENUN ta bakin sakataran hulda da jama'arta Soumaila Zakari Assoumana, ta bayar da shawara ga gwamnati a game da wannan mataki na bayar da horon aikin soja ga masu aikin hidima.
Karin bayani: Tiani ya juya wa yarjejeniyoyin tsaro da waje baya
Ya ce: "Abu ne da aka yi shi shekaru 30 da suka wuce . a loakcin, an samu matsaloli da yawa wadanda suka kai wasu suna rasa rayukansu wajen horon. Don haka, muna kira ga gwamnati ta yi la’akari da irin matsalolin da aka samu a baya kar su sake faruwa a nan gaba. Sannan kuma, muna kira ga gwamnati da ta yi adalci ta kuma fake wajen ganin wadanda suka samun wannan horo, sun samu aiki."
Fa'idar horas da masu yi wa kasa hidima ga kasa
Shi kuwa Abbass Abdoulmoumouni, wani masani kan harkokin tsaro a Nijar cewa ya yi, matakin bayar da horon soji ga masu aikin yi wa kasa hidima zai bai wa kasar damar samar da karin mutane a rundunar ko ta kwana ga kasar. Ya ce: "Na daya, mutanen da ake dauka bautar kasa dubunnai ne kowace shekara. Kenan za a iya samu a yi wata runduna ta ko ta kwana. Idan ta baci ana iya daukar wadanda suka fi kwarewa a kai su fagyn daga ko kuma a sanya su aikin gyara da wanke bindigogi da dai sauran ayyukan a yanayin ta baci"
Karin bayani: Nijar: Horar da matasa kan dimukuradiyya
Sai dai gwamnatin ta ce matakin bayar da horon aikin sojin ba zai shafi wadanda suka rigaya suka soma aikin yi wa hidimar kasar a yanzu ba. Amma kuma, baya ga ma’aikatu da kamfanonin gwamnati, za a dinga tura masu yi wa kasa hidima a kamfanoni da kungiyoyi masu zaman kansu da ma kungiyoyin kasa da kasa da suka shigar da bukata.