1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta haramta fitar da dabbobi kasashen ketare

May 11, 2025

Ma’aikatar bunkasa kasuwanci ta Jamhuriyar Nijar ta sanar da haramta fitar da dabbobi daga kasar zuwa kasashen ketare domin kauce wa tashin farashin dabbobi kafin bikin Babbar Sallar.

Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta haramta fitar da dabbobin kasar don sayarwa a ketare gabanin Babbar Sallah
Hoto: Gazali Abdou/DW

Nijar, kasa mai yawan hamada, na daya daga cikin manyan kasashen da ke fitar da dabbobi musamman zuwa makwabciyarta Najeriya da kuma Ivory Coast.

Ministan kasuwanci, Abdoulaye Seydou, ya ce matakin hana fitar da shanu, tumaki, awaki da rakuma an dauke shi ne domin tabbatar da wadatar dabbobi a kasuwannin cikin gida kafin lokacin Sallar Layya da za a yi a farkon watan gobe na Yuni. Ministan ya ce an umarci jami'an tsaro da su "hukunta duk wanda ya karya wannan doka."

A Nijar, kasa da fiye da kashi 90 cikin 100 na al'ummarta Musulmai ne, ana yanka dubban raguna  a yayin Sallar Layya don haka a cewar gwamnatin mulkin sojin kasar akwai bukatar wadatar da gida kafin fitarwa ketare.

Kungiyoyin 'yan ta'adda a Nijar da yankin Sahel na yawan sace dabbobi, wanda hakan ke sa makiyaya su tsere daga kauyukansu kuma farashi ya karu. Baya ga haka, satar dabbobi na daya daga cikin manyan hanyoyin samun kudin shiga ga kungiyoyin 'yan ta'adda kamar Boko Haram, inda mayakansu ke sayar da wasu dabbobi a kasuwannin cikin gida yayin da suke fitar da wasu domin tallafa wa ayyukansu.