1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsamin dangantaka tsakanin Nijar da Mali

March 21, 2023

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun haramta shigo da kaya daga kasar Mali sai dai masana tattalin arziki sun yi gargadin cewa matakin na iya yin illa ga harkokin tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu

Niger Strassenszene Markt
Hoto: AP

Gwamnonin kananan gundumomin Nijar da ke iyaka da kasar Mali sun gargadi 'yan kasuwa da su kiyaye kasuwancinsu wajen sayar da kayan da suka fito daga Mali lamarin da masana tat-alin arziki suka yi gargadin cewa yana iya haifar da koma baya ta fuskar kasuwanci da ci gaban tattalin arzikin kasashen biyu.  

Hoto: Natasha Burley/AFP/Getty Images

Mahamadou Warzagan shugaban gundumar Ayorou da ke yankin Jihar Tillabery mai fama da matsalar tsaro ya yi karin bayani ga manema labarai game da matakin da ya biyo bayan zaman taron majalisar tsaron kasar Nijar da ya umurci dakatar da duk wata hada hadar kasuwancin kayan kasar Mali a kasuwannin Niger.

To ko wane tasiri hakan ke iya yi a fuskar tattalin arziki Madame Duka kwararriya kan tattalin arziki da ke jami'ar Damagaram ta ce matsalar da matakin zai iya kawowa shi ne kara hadasa talauci.

Kananan yan kasuwa sun yi kira ga gwamnati ta dauki matakin maye gurbin da aka rasa, don kauce wa jefa jama'a cikin mawuyacin hali.

Hoto: Getty Images

Haka su mai dai kungiyoyin fararen hula masu yaki da tsadar rayuwa ta bakin Sadat Iliya Dan Malam na ORCONI sun soki matakin wanda ta ce zai raba kan kasashen Afirka maimakon hada kawunansu wuri daya musaman ta fanin tattalin arziki da zamantakewar yau da kullum,

Mu a gurin mu abun Allah wadarai ne yayin da muke fafutukar ganin cewa wadannan kasashe biyu sun hada karfi da karfe don yakar rashin tsaro da ke damun mu, babu wani wanda zai ci amfanin wannan abun face wadanda suke ganin miyar su tayi tsami a Mali kuma suke son ganin dole sai sun hada rigima tsakanin Mali da suran kasashe. Masana dai na fargaban yadda farashin kayayyaki zai yi tashin gwauron zabi.