1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta kamo fursunonin da suka tsere a yammacin kasar

July 15, 2024

Bayanai da ke fitowa daga Jamhuriyar Nijar, sun tabbatar da kama wasu daga cikin daurarrun da suka kubuce daga babban gidan yarin yankin Tillabery a makon da yagabata.

Hoto: STR/AFP/Getty Images

Hukumomi a Nijar sun sake kamo fursunoni da dama cikin wadanda suka tsere daga gidan yarin  Koutoukale mai tsananin matakan tsaro a cikin jihar Tillabery.

Wasu bayanai dai na cewa an ma kashe wasu daga cikin fursunonin da suka arce a ranar Alhamis.

Gidan yarin dai na dauke ne da daurarrun da suka aikata laifuka na ta'addanci da ma sauran wasu manyan laifukan.

Rundunar sojin kasar ta Nijar ta kuma ce ana ci gaba da neman sauran daurarrun da suka tseren, bayan kafa dokar hana zirga-zirga musamman domin neman su.

Jamhuriyar Nijar dai na karkashin ikon mulkin soji ne, bayan kifar da gwamnatin dimukuradiyya a karshen watan Yulin bara.