1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Nijar ta kori Amurka saboda barazanar takunkumi a kan Iran

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
May 15, 2024

Nijar dai kori sojojin Amurka da suka yada sansani a Agadez, sannan ta katse alaka da uwrgijiyarta Faransa, yayin da a gefe guda kuma ta rungumi Rasha

Hoto: Carley Petesch/AP Photo/picture alliance

Jamhuriyar Nijar ta ce babban dalilin da ya sanya ta katse alakar tsaro da Amurka shi ne yadda kasar ta yi barazanar kakaba mata takunkumi matukar ta kulla alakar cinikayyar ma'adanin Uranium da Iran.

A yayin tattaunawarsa da jaridar Washington Post, firaministan kasar Ali Mahaman Lamine Zeine, ya ce mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amurka mai kula da Afirka Molly Phee ce ta yi wannan gargadi, lokacin da ta jagoranci tawagar Amurka zuwa Nijar domin daidaita al'amura bayan tsamin dangantaka.

Karin bayani:Rasha ta aikewa Nijar makaman kakkabo jiragen yaki da sojoji

Nan take kuma Lamine Zeine ya mayar mata da martanin cewa babu ta yadda za a yi ta je har kasarsu ta ci musu fuska da barazanar sanya takunkumi haka kawai, har ma take tsara musu wadanda ya kamata Nijar din ta yi hulda da su, ta hanyar amfani da kalamai na gadara, wannan ba abu ne da Nijar din za ta taba karba ba, in ji Ali Zeine.

Karin bayani:'Yan Nijar sun yi zanga-zanga neman ficewar sojojin Amurka

Ko da aka tuntubi mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Vedant Patel game da kalaman firaministan Nijar bai musanta abin da ya fada ba, yana mai cewar bukatar da Molly Phee ta gabatarwa Nijar din matsaya ce ta gwamnatin Amurka.

Karin bayani:Gwamnatin sojin Nijar ta soke yarjejeniyar soja da Amurka

Nijar dai kori sojojin Amurka da suka yada sansani a Agadez, sannan ta katse alaka da uwrgijiyarta Faransa, yayin da a gefe guda kuma ta rungumi Rasha, wadda a baya-bayan nan ma ta aike mata da sojoji da makamai domin bai wa sojin Nijar horo.