1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yawan mutanen da suka rasa rayukansu a Saudiya na karuwa

Abdoulaye Mamane Amadou/LMJSeptember 25, 2015

Hukumar da ke kula da aikin hajji ta Jamhuriyar Nijar COHO ta bayyana adadin farko na mutanen kasar da suka rasa rayukansu sakamakon hadarin da ya afku a Saudiyya.

Hadarin Saudiya ya halaka mutane masu yawa
Hadarin Saudiya ya halaka mutane masu yawaHoto: Getty Images/AFP/M. Mahmoud

Hukumar ta ce za su ci gaba da gudanar da kwararan bincike zuwa gaba domin bayar da alkalumman karshe mai dauke da cikakken bayani kan adadin. Babban jami'in hukumar COHO mai kulawa da shirya aikin hajjin a Nijar Alhaji Kadi Abdullahi ya tabbatar da cewar ya zuwa yanzu mahajjatan Jamhuriyar Nijar akalla 19 ne suka rigamu gidan gaskiya a yayinda wasu kuma 7 suka jikkata a hadarin da ya abku a kasar Saudiyan.

Jigilar marasa lafiya zuwa asibitiHoto: Reuters/Saudi Red Crescent

Hankula sun karkata Saudiya

Kalaman na Abdullahi na zuwa ne yayin da hankulan alummar Nijar ya karkata zuwa kasar ta Saudiya bayan jin abubuwan da suka faru, wanda ke zaman na farko mafi muni da suka shafi al'ummar ta kasar. Hukumar ta ce ta samu alkalumman daga hannun wakilanta da suke kasar ta Saudiya wadanda suka je aikin hajjin wannan shekarar. Hukumomin dai sun ce suna ci gaba da kokarin jin labarin sauran jama'ar da suka bace da kara tan-tance adadin wadanda suka jikkata ta hanyar kamfanonin dillancin sufurin alhazai kimanin sama da 20 da ke aikin hajjin na bana.

Mahajjata sun ci gaba da ibadarsu

Yanzu haka dai mahajjatan Jamhuriyar ta Nijar na ci gaba da aikin ibadar su a kasar ta Saudiya. Alhaji Nouhou Mouhamadou Arzika dan gwagwarmayar kungiyoyin fararen hula ne da ke kare hakkin dan Adam da yanzu hakan yake tare da mahajjatan Nijar din a birnin na Mina ya ce lallai akwai wadanda suka ji tsoro kadan da shakkun zuwa jifan shedan sakamakon abin da ya faru a ranar Alhamis, to amma daga karshe an samu nasarar kwantar musu da hankali. Wannan dai shi ne karo na farko da mahajjatan Nijar suka taba tsintar kansu a cikin wannan lamari bayan shafe tsawon shekaru suna aikin hajji a kasar ta Saudiya

Kokarin ceto wadanda ke da sauran numfashiHoto: picture-alliance/dpa/Saudi civil defence agency
Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani