Nijar ta sake samun tallafin tsaro daga Rasha
May 5, 2024Rahotanni sun yi nuni da cewa tawagar farko ta mashawarta kan sha'anin tsaro 10 sun isa kasar ne a ranar 10 ga watan Afrilun 2024 tare da wasu na'urorin tsaro na sama. Ko a ranar Asabar wasu manyan jiragen yaki biyu sun isa kasar. A yanzu Rasha ta turo wa Nijar jiragen saman dakon kaya na yaki guda uku dauke da kayayyakin yaki da kuma masu horo.
Karin bayani:Sojojin Rasha sun canji na Amurka a Nijar
A ranar Alhamis din da ta gabata ce dai, sakataren tsaron Amirka Lloyd Austin ya ce an Rasha ta girki dakarunta a wani sasanin soji da ke kusa da filin jirgim sama na Yammai, inda nan ma akwai dakarun Amirka.
Tun bayan da sojoji suka kwace mulki da kasar a shekarar 2023, Nijar ta kori dakarun Faransa da ke zama uwargijiyarta tare da datse yarjejeniyar tsaro tsakaninta da Amirka.