NIjar ta sauya sunayen wasu manyan tituna na birnin Yamai
October 16, 2024Sojoji sun ta kade-kade domin raya jaruman kasar Nijar a wajen bikin kaddamar da sabbin sunayen tituna da wuraren tarihi na kasar Nijar. Hukumomin mulkin soja sun fara ne da sauya sunaye hudu inda titin Charles De Gaulle tsohon shugaban Faransa ya koma Titin Djibo Bakari wani dan gwagwarmayar samar da ‘yancin kan Nijar, Dandalin Kanal Monteil ya koma Dandalin Thomas Sankara, yayin da Dandalin Farancophonie ya koma Dandalin AES.
Karin bayani: 'Yan fafutuka sun yi nasara kan sojojin Faransa
Brigediya Janar Abdou Assoumane Harouna da ke zama gwamnan birnin Yamai ya bayyana manufar wannan shiri, inda ya ce an yi shi ne da nufin daukaka sunayen jaruman Nijar da na Afirka. Sai dai Farfesa Mamoudou Djibo wani malamin tarihi a kasar Nijar, ya ce shirin ba ya nufin goge alamun mulkin mallaka, amma don kawo gyara ga tarihin kasar. Amma hatta a tsakanin ‘yan kasar NIjar, akwai sabanin ra’ayi kan muhimmanci da kuma dacewar daukar wannan mataki na sauya sunayen titunan birnin Yamai,
Karin bayani: Nijar ta sanar da katse alaka da kungiyar kasashen rainon Faransa OIF
Mahukuntan birnin Yamai suka ce baya ga wadannan wurare hudu da ke zama somin tabi , matakin zai shafi manyan titina da wuraren tarihi wadanda ke dauke da sunayen Turawan mulkin mallaka na Faransa