1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Nijar ta yi tayin hako ma'adanin uranium ga kamfanonin Rasha

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
November 14, 2024

Nijar ce ta 7 a duniya a arzikin uranium, kuma tun bayan juyin mulkin da sojojin suka yi a cikin watan Yulin bara suka raba gari da uwargijiyarsu Faransa.

'Yan dauke da tutar kasarsu da ta Rasha
Hoto: AFP/Getty Images

Jamhuriyar Nijar ta gayyaci kamfanonin Rasha zuwa kasar don gudanar da aikin hakar ma'adanin uranium da ma sauran albarkattun karkashin kasa, kamar yadda ministan ma'adanan kasar Ousmane Abarchi ya nema.

Karin bayani:Gwamnatin Nijar ta gargadi kamfanin ORANO

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya rawaito Mr Abarchi na cewa tuntuni suka gana da da kamfanonin da ke da sha'awar zuwa kasar don fara ayyukansu na hakar ma'adanan, ba wai uranium kadai ba, yana mai cewar babu damar barin kamfanonin Faransa su ci gaba da aiki a kasar, tunda ta nuna rashin amincewarta da gwamnatin mulkin sojinsu.

Karin bayani:Sojojin Rasha sun canji na Amurka a Nijar

Jamuhiyar Nijar ce ta 7 a duniya a arzikin uranium, kuma tun bayan juyin mulkin da sojojin suka yi a cikin watan Yulin bara suka raba gari da uwargijiyarsu Faransa, tare da fatattakar kamfanoninta da ke aiki a kasar.