1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin Faransa a Jamhuriyar Nijar

Salissou Boukari SB/USU
October 4, 2023

Hukumomin mulkin soja na Jamhuryar Nijar suna ci gaba da zargin da suka saba kan kasra Faransa na yunkurin kawo cikas kan tafiyar da kasar da ke yankin yammacin Afirka.

Jamhuriyar Nijar I Zanga-zanga goyon bayan sojojin da suka yi juyin mulki
Zanga-zanga a JAmhuriyar NijarHoto: Balima Boureima/AA/picture alliance

Da yammacin jiya Talata Firaminista Ali Mahaman Lamine Zeine na Jamhurtiyar Nijar, ya gana da kungiyoyin Maluman adinai, yan kungiyoyin fararan hula, da na sarakunan gargajiya, inda ya sanar da su halin da ake ciki a kasar dangane da zargin cewa kasar Faransa na kitsawa da zimmar wargaza kasar ta Nijar ta sabili da cewa sabin hukumomin na mulkin soja sun nemi da sojojin Faransa dubu uku da dari biyar (3500) sun fice daga kasar wanda hakan bai yi wa kasar ta Faransa dadi ba.