1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Takaddama kan kwamitin kwaskware dokokin zabe

October 26, 2016

'Yan adawa sun zargi gwamnatin Shugaba Mahamadou Issoufou da kokarin amfani da wannan mataki don neman makalewa a kan madafun iko.

Niger Amtseid des neu gewählten Präsidenten Mahamadou Issoufou
Hoto: Getty Images/AFP/B. Hama

Duk da yake dokar bata fayyace takamaiman dokokin da suka shafi tsarin zabe da ke kunshe a cikin kundin tsarin mulkin kasar ba da sabon kwamitin ke son ya dukufa a kansu don kawo masu gyaran fuska
 

Sabuwar dokar da ofishin ministan cikin gida ya dauka kuma aka saka wa hannu tun a ranar 14 ga wannan watan Oktoba, ta ambaci nazarin sake fasalta dokar zaben 'yan majalisun dokoki da na shugaban kasa da ma dokar gundarin shirya zaben kasar, kan kanta uwa uba da na kundin tsarin mulki wanda ambaton shi a cikin jadawalin ke ci gaba da tayar da hankalin wasu 'yan kasar da ke zargin gwamnatin da shirin amfani da damar da take da don yiwa kundin tsarin mulkin kasar mai ci yanzu gyaran fuska da zummar kara makalewa a wani sabon wa'adi na mulki ta hanyar sake fasalin mulki daga tsarin mulki mai ruwa biyu zuwa wani tsari na shugaban kasa mai cikakken 'yanci.

Dan takarar da ya sha kaye a zaben shugaban kasa na watan Maris a karkashin inuwar Model Ma'aikata Alhaji Tahirou Guimba kuma daya daga cikin masu adawa da manufofin shugaban kasa ya ce ba tun yau ba suka kwan da sanin cewar hakan na iya faruwa daga gwamnatin ta "Renaissance".

"Duk mun ji take-taken nan da ma gwamnatin don a canja kundin tsarin mulki ne a je "Referendum", akwai ma wata tazarce a ciki. To wanda duk ya ce yana iya hade gatari sai ka rike mashi bota, don dahuwar da ake yi a kasashen waje ba za a iya yinta a Nijar ba. Mutum da ya hau mulki sai ya yi zaton kamar shi kadai ne, bayan shi babu wani dan Nijar da Allah Ya yi da zai hau mulki ba kuma?"

Dan takarar ya ci gaba yana mai cewar tun da jimawa fasalin tafiyar da ikon kasar ya canja zuwa ga sabbin manufofin gwamnatin mai ci yanzu, daga tsarin mulki na rarraba iko ga jam'iyyu zuwa wato tsarin mai ruwa biyu zuwa ga wani tsari irin na tuwona maina, wato shugaban kasa mai cikakken 'yanci duba da yadda daukacin manyan mukaman kasar suka makale ga jam'iyyar da ke mulki.

"Shugaban kasa dan tarayya ne, shugaban majalisa dan tarayya ne, firaminista dan tarayya ne, da ministocin kasa masu muhimmanci shida, duka 'yan tarayya ne. Kenan an canja tsrin mulki tun da jimawa an kare mutane mafalki ne suke yanzu takardu kawai za a yi."

Sai dai kwamitin ya nisanta kansa da niyar nazari don canza kundin tsarin mulki na kasa yana mai cewar dokokin zaben Nijar ne suka kasance da sarkakiya, duba da muhimman tarurrukan da aka sha yi a baya inda aka bukaci da a sake ingantasu, sakamakon kai ruwa rana da aka yi ta yi a zabubbukan shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki da ma suka kai ga 'yan adawa janye takararsu saboda zargin rashin adalci.

Malam Yahaya Garba kakakin kwamitin ne da ke wakiltar hukumar CNDP.

"Dole ne idan aka ce dokokin zabe dole a yi maganar kundin tsarin mulki, shi kuma kundin kansa matsalolinsa kowa ya sani wa'adin kwanaki ne da tsarin doka "loi organique" ko "loi semple" shi ne kawai za a gyara abu biyu wannan ai kuma ba kundin tsarin mulkin kadai ba ne, da shi da sauran wasu dokokin zabe su ne za a yi. Kenan duk wani zancen za a gyara kundin tsarin mulki ba dai daga wannan kwamitin ba."

A ka'idance kwamitin zai shafe tsawon kwanaki yana aikin ne kan daga bisani ya aika rahotonsa ga ministan cikin gida a yayin da a share daya hukumar ta CNDP za ta kara kafa wani kwamitin don nazarin fasalin kafin tura dokar ga majalisar dokoki don jefa mata kuri'a.

Sai dai har yanzu wasu 'yan kasar sun yi imani da cewar idan ba niyyar sake fasalta kundin mi ya kawo maganar sauya wasu daga cikin dokokinsa a yanzu, duba da wani taron da kwararrun tsarin mulki ke yi yanzu haka kan batun tsarin mulki mai ruwa biyu.

Kundin tsarin mulki dai ya halatta yin gyaran fuska ga kundin muddin kashi 3/4 na 'yan majalisa suka jefa kuri'ar amincewa da haka. Sai dai kundin ya kuma haramta canjawa da ma yin gyaran fuska ga doka mai lamba 47 da ta kayyade wa'adin mulkin shugaban kasa komai rintsi komai wuya.

Ginin fadar Shugabgan kasar NijarHoto: DW/M. Kanta
Wani jerin gwanon 'yan adawa a birnin YamaiHoto: DW/M. Kanta