Nijar: Tchiani ya sauke ministan mai na kasa
January 7, 2026
A wani kudirin doka da shugaban gwamnatin mulkin soja shugaban kasa Janar Abdourahamne Tchiani ya dauka ya nada Malam Hamadou Tinni kwararren masanin dokoki da bincike a harkokin kudi da haraji a matsayin sabon ministan man fetur na kasar inda ya maye gurbin Dr Sahabi Oumarou, kasa da watanni 17 da nadashi kan wannan matsayi domin maye gurbin ministan man fetur na farko na gwamnatin Tchiani Malam Barke Bako Mahaman Moustapha wanda aka tsige tare ma da kama shi a ranar 25 ga watan Janerun 2025.
Karin Bayani: Nijar ta sanar da dakatar da tura danyen man fetur dinta zuwa Benin
To ko wace fassara za a iya yi wa wannan sauye-sauyen ministoci a ma'aikatar man fetur ta kasar inda aka nada ministoci uku a cikin kasa da shekaru uku?.
Babu dai wani bayani da gwamnatin ta yi a game da dalilan yawan tsige-tsigen ministocin man fetur din da kuma nade-naden sabbi. A kan haka ne Malam Ismael Mohamed wani dan fafutika a Nijar ya ce akwai bukatar daukar matakin kauce wa tabbatuwar canjin da aka yi wa man fetur na kasancewa tushen fitina a kasa.
Karin Bayani:Nijar: Sabon takun saka da kamfanonin mai na China
Nadin sabon ministan man fetur din na kasar Nijar na zuwa ne a daidai lokacin da kotu ta wanke sohon ministan man fetur na kasar Malam Barke Bako wanda aka tsige tare da tsare shi kusan watanni 11 a kurkuku.
Yanzu dai jama'a sun zura ido su ga kamu ludayin sabon ministan man fetur din na kasa suna cike da fatan ganin zai yi nasarar shawo kan matsalolin da suka dabaibaye harkar man fetur na sabani tsakanin Nijar da China da hare-haren ‘yan tawaye kan bututun mai da kuma badakalar da ake zargin an kwashe shekaru ana cuwa-cuwa a harkar man fetur a kasar.