1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Yaki da sayar da naman bayan fage a Nijar

May 21, 2019

A wani mataki na rigakafin yaduwar cututuka da ake kamuwa da su ta hanyar cin nama maras kyau, hukumar kula da aikin nama a Damagaram ta kaddamar da samamen kamen mahauta masu sana'ar nama ta bayen fage.

Uganda Fleish wird mit Formaldehyd behandelt
Hoto: DW/F. Yiga

A Jamhuriyar Nijar a wani mataki na kare lafiyar al'umma daga aukawa cikin bala'i bayan cin nama maras kyau da ke shigowa kasuwanni ta barauniyar hanya ko yankan gida da wasu mahauta ke aikatawa, hukumar kula da tsaptar nama cewar kwata a jihar Damagaram ta kaddamar da rangadin yaki da wanan matsala a daidai lokacin da al'umma ke cikin bukatar nama bayan buda baki. Tuni dai hukumar ta bayyana cewar ta fara sa hanu a kan irin wadanan mahauta masu yankan gida inda kuma ta yi alkawarin ladabtar da su ta hanyar doka.

Wanan samame dai da jami’an hukumar kwata gami da ta lafiyar dabobi suka kai a lungu da sako na birnin na Damagaram domin bankado mahautan da ke aiwatar da yankan gida ba shi ne na farko ba a cewar dokta Madugu shugaban ma’aikatar lafiyar dabbobi wanda ya ce tuni wasu daga mahautan da ke yankan bayan fagen suka shiga hannu kuma za a hukunta su a daidai tanajin da doka ta yi kan masu aikata irin wannan laifi.

Hoto: DW/F. Yiga

Ousseini Saley sarkin fawar Damagaram da ake gudanar da aikin samamen gano masu yankan gidan cewa ya yi matakin da mahukuntan suka dauka ya yi daidai, domin kuwa babu mahaucin da bai san da wannan doka ba wacce ta haramta yankan na bayan fage. Sannan ya kara da cewa yankan gida na durkusar da sana'ar hawa ta la'akari da yadda wasu mahautan ke kashe kudi wajen sayan dabbar yankan a yayin da shi mahaucin bayan fage ke sayanta da arhar da ke jan hankalin masu dan karamin karfi. Lamarin da ke sanyawa masu yankan gidan ke cin ribar da ta wuce ta mahaucin da ya kiyaye ka'ida wajen yankan bisar da sayar da namanta.

Jama'a da dama dai sun bayyana gamsuwarsu da wannan mataki wanda suka ce zai taimaka wajen hana jama'a kamuwa da cututuka da ake dauka ta hanyar cin naman bisar maras lafiya. Kawo yanzu dai hukumomin sun kafa dokar haramta shigo da yankakun
bisashe kasuwanni daga karkara har sai an kai naman kwata an tabbatar da lafiyarsa.