1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan tawayen masu fafutikar dawo da gwamnatin Bazoum sun tuba

Abdoulaye Mamane Amadou ATB
November 12, 2024

Mayakan kungiyar 'yan tawaye da ke hankorin a dawo da gwamnatin Mohamed Bazom da sojoji suka hambarar a Nijar sun mika wuya, tare da jingine makamai a yankin arewacin kasar.

Hoto: Getty Images/AFP

Mutanen tara da ke karkashin wata kungiyar mai suna Front Patriotique de Libération (FPL) da wani tsohon dan tawayen da ya taba tuba Mahmoud Salah ke jagoranta sun jingine makamai ne a yayin wani kaiasitaccen bikin da aka gudanar a fadar gwamnatin yankin Agadez da ke arewacin Nijar.

Karin Bayani : Laluben hanyoyin inganta shari'a a Nijar

A makon da ya gabata wasu kusoshin kungiyar da suka hada da kakakinta Idrissa Madaki, da wasu barade uku sun tuba tare da mika wuya da makamai kan abin da suka kira neman samar da zaman lafiya.

Karin Bayani : Nijar: Bukatun al'umma a kan gwamnati

A baya kungiyar da dauki alhakin kaddamar da jerin hare-hare a wurare da dama na Nijar ciki har da wani hari akan bututun dakon danyen man fetur da kai wani hari tarin da ya yi garkuwa da kantoman Bilma a yankin arewacin Nijar.