1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Yunkurin magance matsalar tsaro a Nijar

Salissou Boukari RGB
February 6, 2023

Ministan kula da harkokin cikin gida tare da rakiyar shugabannin jami'an tsaro sun isa a garin Abalak domin tattauna hanyoyin samun zaman lafiya.

Shugaba Bazoum na kokarin shawo kan matsalar tsaro
Shugaba Bazoum na kokarin shawo kan matsalar tsaroHoto: Presse- und Kommunikationsdienst der Präsidentschaft von Niger

A jamhuriyar Nijar a wani mataki na neman zaman lafiya mai dorewa a yankunan jihar Tillabery, Ministan kula da harkokin cikin gida tare da rakiyar shugabannin jami'an tsaro sun isa a garin Abalak da ke da nisan kilomita kimanin 60 da Yamai, babban birnin kasar ta Nijar domin tattauna hanyoyin samun zaman lafiya da shugabannin al'ummomi na yankin, musamman dangane da wasu alkawura da suka dauka a baya na bayar da gudunmowa a fannin samun zaman lafiya.

Tun da hawan kan karagar mulkin kasar ta Nijar, Shugaba Mohamed Bazoum ke fatan ganin ya yi amfani da hanyoyi na tattaunawa a fannoni da dama wajen shayo kan matsaloli har ma da wannan fanni na matsalar tsaro da ake fuskanta a cikin yankuna da dama na jihar Tillabery, yara da dama suka shiga cikin wannan aiki na ta'addanci bayan da aka tilasta musu ko kuma aka yi musu mugunyar huduba.

Ta haka a kwanakin baya ya yin wata tattaunawa da hukumomin na Nijar, jagororin al'umma na yankunan Abalak da ke jihar ta Tillabery da ma wasu yankuna na jihar Tahoua, sun dauki alkawura na kawo taimako a shayo kan matsalar ta tsaro.

Abun jira a gani, shi ne mataki da su wadannan shugabanni na al'ummomin karkara za su dauka nan zuwa wani lokaci domin sanyaya zukatan mahakuntan kasar ta Nijar da ke fatan ganin an samu kwanciyar hankali mai dorewa ta hanyar tattaunawa.