1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Za a ci gaba da tsare Hama Amadou

Mahaman Kanta/ MNAJanuary 11, 2016

Kotun daukaka kara ta birnin Yamai ta yi watsi da bukatar neman beli ga shugaban jam'iyyar Lumana Afrika kana dan takararta a zaben shugaban kasa wato Malam Hama Amadou.

Hama Amadou nigrischer Oppositionspolitiker
Hoto: DW/S. Boukari

Dubban magoya bayan jam'iyyar Lumana Afrika ta Hama Amadou da ma sauran wasu jam'iyyun adawa suka yi cincirindo a harabar kotun don jin yadda za ta kaya. Sai dai hankali ya tashi da jin cewa an yi watsi da maganar yi wa shugaban na Lumana beli. Wata mai goyon bayan Hama Amadou ta barke da kuka lokacin da aka bayyana hukuncin.

"Sau dubu ana tsare Hama ina baya gare shi. Kuma Hama ya kwantar da hankalinshi ko yana kaso ka ba shi kaso, mu wannan bai samu tsoro mu fita bayan Hama."

Bankana Mai Fada tsohon dan majalisar dokoki kuma jigo a jam'iyyar Lumana Afrika din ta Hama Amadou da ke cikin jerin jama'a da suka yi cincirindo a kotun ya yi tsokaci a kan hukuncin.

"Yanzu za mu yi na'am da sakamakon kotu. Domin mun san da yardar Allah wata rana gaskiya za ta yi galaba a kan karya. Mu dai mun sa cewa dan takararmu ne, za mu ci gaba da aiki da takararshi yadda ya kamata. Za mu yi gwagwarmaya don Hama ko da an tsareshi, ya fito da mukamin shugaban kasar Nijar."

Takaicin rashin ba wa Hama Amadou beli

Ita dai badakalar cinikin jarirai da ake tuhumar Hama Amadou da ita, ta shafi mutum sama da 30, wadanda dukkannin sauran suna a waje. A dangane da haka Ibrahim Bana wani kusa a jam'iyyar ta Lumana Afrika din ya nuna takaicinsa a kai.

Mahamadou Issoufou da Hama AmadouHoto: BOUREIMA HAMA/AFP/Getty Images

"Duk wanda ke kallon al'amuran siyasa a Nijar ya san da wata manufa ake tsare da shi. Sun san tun da suka wa Hama Amadou wannan zargin, mutane sun gane lalle ba a son a barshi ya je zabe. Wannan kuma yana karfafa jam'iyyarmu. A kullum mutane na fita daga bangarorin jam'iyyunsu suna shiga cikin Modem Lumana. Haka aka yi wa Mahamadou Issoufou rashin adalci lokacin tazarce, ba ga shi ya zama shugaban kasa ba? Shi yasa wannan rashin adalci da ake wa Hama Amadou shi za sa 'yan Nijar sun jefa masa kuri'a kuma ya zama na farko a zaben watan Fabrairu."

Kasancewa lauyoyi a Nijar suna yajin aiki a wannan Litinin, ba a san dalilan da suka sa aka yi watsi da belin ba. Shi dai Hama Amadou na daga cikin mutane 15 da kotun kolin tsarin mulki ta amince da tsayawarsu takara a zaben 21 ga watan Fabrairu 2016. A Nijar dai ba farau ba mutum ya kasance cikin kaso amma ya tsaya takara ya ci zabe. A zabukan da suka gabata an samu wasu 'yan majalisar dokoki suna kaso amma sun ci zabe, kuma daga bisani an sallamesu suka dauki mukamansu.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani