1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta samu karin rance daga bankin Afirka

Gazali Abdou Tasawa ZMA
October 2, 2025

Nijar da bankin raya tattalin arzikin kasashen Afirka sun cimma wata yarjejeniyar bashin kudi na sama da miliyan dubu 80 na CFA.

Niger Ali Mahaman Lamine Zeine
Niger Ali Mahaman Lamine Zeine, fraministan NijarHoto: DW

Gwamnatin  za ta yi amfani da kudin domin fuskantar jerin wasu matsaloli na tattalin arzikin da suka dabaibaye kasar a sakamakon kangin da kasashen duniya suka saka mata tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin 2023.

Gwamnatin mulkin sojan ta ce ko baya ga bunkasa harkar makamashi, za ta saka wani kaso na kudin wajen tallafa wa bankuna na kasa da inganta hanyoyin samar da kudaden shiga aljihun gwamnati da kuma biyan basussukan na cikin gida da dai sauransu.

Firaministan kasar Nijar kana ministan kudi na kasa Malam Ali Mahamane Lamine Zeine ya yi tafiyayya ne har zuwa cibiyar Bankin Raya Tattalin Arzikin kasashen Afirka din na BAD ne, domin sanya hannu kan wannan yarjejeniyar bashin kudi miliyan dubu 80 da 900 kwatankwancin miliyan 144,7 na Dalar Amirka.

Sidi Ould Tah, shugaban bankin raya AfirkaHoto: Issouf Sanogo/AFP

Gwamnatin ta ce za ta yi amfani da wannan kudin bashi ne domin ko baya ga bunkasa hanyoyin samar da karin makashi a kasar, za ta inganta da kuma kare hanyoyin samar da kudaden shiga aljihun gwamnati daga ha'incin wasu jami'an cibiyoyin samar da kudi ga kasa.

Wasu alkalumman ma'aikatar kudi ta kasa na shekara ta 2023 sun nunar da cewa kudaden bashi na cikin gida da ‚yan aksuwar kasar ke bin gwamnati sun kai biliyan dubu biyu na CFA. Lamarin da ya gurguntar da harkokin kasuwancin ‚yan kasuwa da dama da kuma ya kai babban bankin kasar na SONIBANK ga kwace manyan gidaje da kadarorin ‚yan kasuwa da dama. To amma gwamnatin ta ce

za ta yi amfani da wani kaso na wannan kudin bashi domin biyan basussukan na cikin gida. Batun da Malam Tchambiano Chaibou na babbar kungiyar, yan kasuwan Nijar masu shigo da kaya daga ketare ya ce abin farin ciki ne a gare su.

Janar Abdourahamane Tiani, shugaban NijarHoto: Boureima Hama/AFP

Gwamnatin ta Nijar ta kuma ce z ata yi amfani da wani akso na wannan kudi da ta ciyo bashi domin bunkasa harkokin cinikayya da kuma zawarcin masu saka jari na ketare zuwa cikin kasar. Matakin da Malam Aissami Tchiroma wani mai sharhi kan harkokin tattalin arziki ya ce zai taimaka ga farfado tattalin narzikin kasar daga komabayan da yake fuskanta.

Sai dai wasu masana ilimin tattalin arziki na ganin akwai bukatar Nijar ta kara ciwo bashin wasu makwadan kudaden idan har tana son tunkarar matsalolin tattalin arzikin da suka dabaibaye ta domin kuwa wadannan biliyan 80 da ‚yan ka na CFA ta ciyo bashi ba su taka kara sun karya sun karya ba ga bukatar da tattalin arzikin aksar yake da ba.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani