1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar na neman sulhu da mayakan jihadi

Abdul-raheem Hassan
March 18, 2022

Gwamnatin Nijar na ci gaba da shirin tattaunawa da mayakan jihadi da ke addabar yankin kudu maso yammacin kasar, yayin da ake fargabar hare-hare a yankin Tillaberi bayan da Faransa ta sanar da janye dakarunta daga Mali.

Nigeria I Präsidenten Mohamed Bazoum
Hoto: Facebook/Präsidentschaft der Republik Niger

Kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP ya ce wata majiya daga fadar gwamnatin Nijar, na cewa Shugaba Mohamed Bazoum ya fara tuntubar wasu kusoshin kungiyar masu jihadi watanni uku da suka gabata, inda ya yi musu tayin ajiye makamansu don samar da zaman lafiya.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito cewa Shugaba Bazoum ya sako mayakan jihadi da dama da ke tsare a gidajen yarin kasar, ya kuma karbe su a fadarsa tare da tura wakilai don shawo kan sauran shuagbannin kungiyoyin da ke tada kayar baya.

Yanzu haka dai gwamnatin Bazoum ta kara yawan dakarun kasar Nijar daga 11,000 zuwa 30,000, tare da girka 12,000 a rundunar yaki da ta'addanci.