Nijar:An gudanar da bikin a'aldu na makiyaya
September 19, 2017Talla
Bikin Cure Salée dai ko kuma lasa gishiri biki ne da ke hada makiyaya Nijar baki daya, kuma wannan shi ne karo na 54 da ake gudanar da bikin a karkashin jagoranci firaministan Nijar Birji Rafini. Makiyayan dai kan yin amfani da wannan dama domin nuna al'adunsu tun daga tufafi, kitso, kafin a yi gasar fitar da sarauniyar kyau da kuma naminji da ya fi kowa kyau a tsakanin makiyayan. Kuma a bana ma an gudanar da bikin ne kamar yadda aka saba a kowace shekara lami lafiya.