Nijeriya: Ganawa da manyan alkalai a fadar Aso Rock
October 6, 2017Kudin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi 'yancin gashin kai a tsakanin bangaren zartarwa dana shari'a, ba kasafai ake ganin alkalai a cikin fadar gwamnatin kasar ba amma sannu a hankali wani danyen ganyen da ake ta'allakawa da mayar da ido ga bangaren shari'ar, na neman mayar da alkalan wuce makadi cikin rawa a sabo na kawancen da ke tsakanin su da fadar gwamnatin kasar ta Aso Rock. Ziyarar alkalan ta zamo dama ga shugaban na neman kafa kotuna na musamman a kasar da nufin gaggauta kammala shari'un cin hanci. Shugaba Buhari ya ce akwai bukatar kara kotunan yaki da hanci a matsakaicin tsarin shari'a sannan kuma da ware rana guda a kowane mako domin sauraron shari'un hanci a kotun ta koli dama 'yar uwarta ta daukaka kara.
Ana kallon ziyarar manyan alkalan da suka ce sun isa fadar gwamnatin kasar da nufin barka da zuwa ga shugaban kasar daga nema na magani a matsayin wani abu na ba sabunba, haka kalamai na babban alkalin kasar mai Shari'a Walter Ononghen, wanda da kyar da gumin goshi ya kai ga samun tabbatar da shi a mukamin, alamu na mika wuyar alkalan ne domin yakar cin hanci. Abun jira a gani dai na zaman nisa na hadin kan da kila danyen ganyen a tsakanin gwamnatin da ke kara kusantar zabe da kuma bangaren shari'ar da ke da jan aikin adalci ga batu na zabukan a matakai daban-daban.